Daga Abubakar Isa
Kotun koli ta bayyana zaben kananan hukumomi da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Ribas ta gudanar a ranar 5 ga watan Oktoban 2024 a matsayin haramtacce
A wani hukunci da mai shari’a Jamilu Tukur ya yanke, kotun ta bayyana zaben a matsayin wanda ba shi da inganci, bisa laifin karya dokar zabe.

Da yake karanta hukuncin, Mai shari’a Tukur ya ce matakin da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Ribas ta dauka, ya zama maras amfani saboda rashin bin dokar zabe da ka’idojin zabe yayin da hukumar zaben ta ci gaba da yin rajistar masu kada kuri’a har bayan sanar da ranar zabe.
Rundunar Yansandan Kano ta yi Karin Haske Kan Yunkurin Kone Gidan Sarki na Nasarawa
Kotun ta ce an soke hanyoyin da suka kai ga gudanar da zaben kananan hukumomi wanda hakan ya sabawa sashe na 150 na dokar zabe.