Daga Abdulmajid Habib Isa
Jami’an tsaro sun yiwa gidan Sarkin Kano na Nasarawa kawanya tun da sanyin safiyar Wannan rana ta laraba.
Wakilin Kadaura24 da ya ga yadda aka tsaurara tsaron ya ce ya lura bayan jami’an tsaron dake kula da gidan sarkin, a yau an kara wasu jami’an tsaron masu yawa.
Gidan Sarkin Kano na Nasarawa dai a yanzu a nan Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero yake zaune, tun bayan da gwamnatin jihar Kano ta ayyana cire shi daga Sarautar Kano.
Sai dai Alhaji Aminu Ado Bayero da wasu daga cikin mukarabansa sun garzaya kotu domin kalubalantar matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na cire shi, tare da dawo da Malam Muhammad Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

Lamarin dai ya haura akalla watanni 8 kenan ana fafata shari’a akai wanda kuma yanzu haka bayan hukuncin Kotun daukaka kara, bangaren Sarki Aminu Ado sun garzaya Kotun koli don kalubalantar hukuncin da kotu ta yanke.
A wannan rana ta laraba ne dai aka wayi gari da ganin karin jami’an tsaron wadanda suka rufe hannun da gidan sarki na Nasarawa yake wanda yake kan titin zuwa gidan gwamnatin jihar Kano.
Da dumi-dumi: Ma’aikatan hukumar samar da ruwa ta Kano sun tsunduma yajin aiki
Kadaura24 ta rawaito jami’an tsaron sun rufe hanyar ne tun daga kan gadar kofar Nasarawa da duk wata hanya da za ta sada mutum da gidan Sarkin.
Sai dai daga bayan sun bude wasu daga cikin hanyoyin, kuma yanzu haka ma ana bin hanyoyin.
Wakilin na mu ya shaida mana cewa a binciken da yayi ya gano cewa hakan na da Nasaba da ikirarin kune gidan Sarkin da wasu matasa suka shirya yi.
Wasu da na zanta da su sun bayyana min cewa ” Rufe hanyoyin gidan Sarkin yana da alaka da kokarin da wasu matasa suka yi na kone gidan Sarkin, domin wai sarki Aminu Ado Bayero ba shi da hurumin zaman a Kano tun da ba shi ba ne Sarkin Kano”.
Har yanzu dai ba wani bayani daga hukumomin tsaro game da rufe hanyoyin gidan Sarkin.
Bayan ya samu ya shiga gidan Sarkin, wakilin Kadaura24 ya gano cewa Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ba ya gari ya yi tafiya zuwa Binin.