Gwamnan jihar Kano Eng. Abba Kabir Yusuf ya gargadi malamai da su daina tilastawa dalibai yin aikace-aikace masu wahala a ciki ko a wajen makaranta
Haramcin na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sunusi Bature Dawakin-Tofa, ya aikowa Kadaura24 .
Gwamnan ya jaddada cewa makarantu wuraren karatu ne na koyar da ilimi da tarbiyya, ba wuraren yin aikin wahala ba.

Yayin wata ziyarar bazata da ya ka makarantar koyon harshen larabci (School for Arabic Studies) Kano, gwamnan ya tarar da wasu dalibai suna tonon ramin bututun bayan gida.
Inda cikin fushi, gwamnan ya tambayi shugaban makarantar dalilin da ya sa aka ba dalibai irin wannan aiki.
Shugaban makarantar ya shaidawa gwamna cewa aikin an ba su ne bayan an tashi daga makaranta.
Zargin batanci: Kotu ta aikewa Abdullahi Abbas da Faizu Alfindiki sammaci
Sai dai nan take gwamnan ya bayar da umarnin dakatar da yaran da aka sa aikin, ya kuma tabbatar wa shugabannin makarantar cewa gwamnatinsa za ta gyara dukkan gine-ginen da suka lalace, har da masallacin da ke cikin makarantar.
Haka kuma, ya bada umarni cewa duk wata bukata ta gyaran makaranta a mikata ga Ma’aikatar Ilimi ko ofishinsa domin aiwatarwa.