Daga Musa Mudi Dawakin Tofa
Sanannen Dankasuwar nan a Kano Alhaji Ibrahim Danyaro, ya yi alkawarin daukar nauyin karatun marayu 20 domin inganta rayuwarsu.
Alhaji Ibrahim Danyaro ya bayyana hakan ne ya yin gabatar da taron walimar sauka da haddar littafin Alkur’ani na dalibai 51, a makarantar Almadina Tahafizul Qur’an dake garin Dawakin Tofa a ranar Lahadi.
Alhaji Danyaro, ya bukaci a zabo masa dalibai marayu 20 a makarantar Almadina wadanda zai dauki nauyin karatunsu har zuwa matakin sauke littafin Alkur’ani mai girma.

“Ya kara da cewa zai baiwa daliban makarantar Almadina da suka yi sauka da haddar Alkur’ani hadi da malamansu tallafin gudunmawa ta naira dubu dari biyar-biyar”
Wakilin mai masaukin baki a taron mai girma mataimakin shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Ubale Magaji Aliyu, bayan taya daliban murna kana ya yi alkawarin baiwa makarantar Almadina gudunmawar naira dubu dari (#100,000) a matsayin sadaka-mai-gudana (sadakatun jariyatun) ga mahaifinsa biyu da suka rasu.
Zargin batanci: Kotu ta aikewa Abdullahi Abbas da Faizu Alfindiki sammaci
Uban taron mai girma Madakin Madakin Kano Hakimin Dawakin Tofa Alhaji Yusuf Nabani Cigari, ya hori iyaye da su kara himma wurin baiwa ‘ya’yansu tarbiyya islamiyya, don a samu cigaba da fita daga halin matsin rayuwar da al’umma ke ciki.
Shugaban gudanarwar gamaiyar makarantun Almadina Sheik Auwal Bin Umar, ya ce an samar da makarantar tun sama da shekaru 25 da suka shude, kuma ita ce Islamiyya daya tilo a garin Dawakin Tofa da aka fara karantar dalbai ilimi a tsarin lokacin karatu na Yamma dukko da cewa akwai tarin makarantun Allo na Yamma da wasu Islamiyyu na Dare a garin.
Kwanaki 100: Shugaban karamar hukumar Wudil ya kaddamar da wasu aiyukan raya kasa
“Ya godewa wasu daga cikin wadanda suka bada gagarumar gudunmawa don tabbatuwar makarantar da bunkasarta kamar sakataren gudanarwar cibiyar kula da harkokin addinin Musulunci ta karamar hukumar Dawakin Tofa Malam Sa’idu Musa, wanda ya jagoranceta sama da shekaru goma sha.
Uban gamaiyar makarantun Alamadina Malam Saminu Sabi’u ya godewa iyaye yara, manyan alaramomi da manyan malamai da kuma manyan baki maza da mata da suka halarci taron walimar sauka da haddar Alkur’ani, a harabar makarantar Model Firamare Dawakin Tofa, Kano.