Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Shugaban hadaddiyar kasuwar kantin kwari dake jihar Kano a arewacin Nigeria Amb. Alhaji Ishaq Alkasim Tatari ya bukaci masu gidaje a kasuwar da su rika rage kudaden da suke karba na haya don saukaka al’umma.
Amb. Ishaq Tatari ya bayyana hakan ne yayin wani taro da kungiyarsu ta shirya don nemawa masu haya a gidajen sauki tare da karrama wasu muhimman mutane a kasuwar ta kwari.

” Mun zauna wannan taro ne domin mun fahimci wasu daga cikin masu gidaje a cikin kasuwar kwari suna karawa masu haya a gidajensu kudi, don haka mu ka ga dacewar mu zauna da su don mu gano a inda gizo ke sakar”. Inji Amb. Tatari
Alhaji Ishaq Tatari wanda kuma shi ne Sarkin Hausawan Arewacin Nigeria ya ce sun fahimci wasu tsiraru ne suke hura wutar, kuma sun gano su, sun kuma fahimtar da masu gidajen.
Zargin Badala: Gwamnatin Kano ta dakatar da daukar wani Fim
” Muna so masu gidajen su sani, Allah ya ba su arzikin da suke da shi domin su taimakawa na kasa da su, muna fatan yadda suka fahimci bayanin da muka yi musu za su sassautawa masu haya a gidajen nasu don cigaban kasuwar da jihar Kano baki daya “.
Ya ce a yayin taron kuma sun karrama wasu daga cikin masu gidaje a kasuwar ta kwari saboda yadda a koda yaushe suke saukakawa masu haya a gidajensu.
Al’ummar unguwar Kan Tudu Sun yabawa Gwamnan Kano bisa Nada Waiya A Matsayin Kwamishina
Alhaji Ishaq Tatari ya kuma ce an karrama wasu daga cikin wadanda suke tallafawa kasuwar ta fannoni daban-daban da kuma wandanda suke kokori wajen samawa matasa aikin yi a cikin kasuwar.
Ya yi fatan nan gaba kadan al’amuran taya za su daidaita tsakanin masu gidajen da wadanda suke haya a gidajensu.