Karanci ruwa: Manoma a Bagwai sun shiga fargaba

Date:

Daga Shu’aibu Bagwai

 

Manoma a wuraren noma na Madatsar ruwa ta Watari da ke karamar hukumar Bagwai a jihar Kano, sun bayyana fargabar ci gaba da fuskantar mummunar asara sakamakon karancin ruwan noma a gonakinsu fiye da shekaru 3 da suka gabata.

Shugaban Kungiyar Manoman yankin, Alh. Ibrahim Sani Janruwa ya bayyana haka lokacin da yake nunawa manema labarai wuraren da matsalar ta shafa.

Alh. Ibrahim Janruwa ya ce a shekaru 3 da suka gabata Bankin bunkasa harkokin addinin Musulunci na duniya ya bayar da tallafin kudi domin fadadawa da kuma gyara hanyoyin ban ruwa a yankin na Watari amma abun takaici wadanda aka damka al’amarin a hannunsu suka nuna son zuciya da cin amana wajen bayar da aikin ga Dankwangilar da ba Shi da kayan aiki, sakamakon haka ya aiwatar da aiki mara inganci wanda maimakon a sami cigaba sai aka sami koma baya mara adadi.

InShot 20250115 195118875
Talla

Shugaban Kungiyar yace a lokacin yarjejeniyar aikin an cimma matsayar cewar cikin watanni 6 Dankwangilar zai kammala aikin amma sai da ya kwashe fiye da shekaru 3 bai kammala ba, kuma zai rika karbar shawara daga manoman amma suka yi biris da ka’idojin yarjejeniyar saboda suna son su yi aiki mara inganci.

Yanzu-yanzu: Gwamna Yusuf ya nada sabon sakataren gwamnatin jihar Kano

Ya ce sakamakon wannan matsala yanzu haka a kalla gonaki fiye da dubu 10 ba sa samun ruwan amfani wanda hakan babbar barazana ce ga zaman lafiya da cigaban tattalin arzikin jihar Kano.

Alh. Ibrahim Janruwa ya kara da cewa yanzu haka kiyasi ya tabbatar da cewa kaso daya ne kawai cikin kaso 4 na adadin gonakin manoma ke samun ruwan amfani.

Shugaban Kungiyar Manoman ya bukaci hukumomi da Kungiyoyin da abun ya shafa su duba wannan matsalar domin kaucewa fadawa cikin mummunan karancin abinci da rashin aikin yi a yankin da Jihar Kano da ma Kasa baki daya, bisa la’akari da gudunmowar da Madatsar ruwa ta Watari da ke Bagwai ke bayarwa wajen samar da abinci da ayyukan yi a Kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu Yanzu: Hukumar KNUPDA ta rushe gaban shagon jarumar Tiktok Rahama

Daga Rahama Umar Kwaru   Hukumar KNUPDA ta kaddamar da rushe...

Wata kungiya ta bukaci Gwamnan Kano ya dakatar da Shugaban karamar hukumar Gwale

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Wata kungiya mai zaman kanta mai...

Kwankwaso ba zai koma APC ba – Buba Galadima

Kusa a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya karyata jita-jitar...

Yadda gwamnan Kano ya ke rabon kujerun aikin hajjin bana kamar gyada

Daga Rahama Umar Kwaru Al'ummar jihar Kano na cigaba da...