Mahalarta Taron “KILAF 24” Sun Yaba da Yadda Kano ta Adana Kayan Tarihinta

Date:

Daga Abubakar Yakubu

 

Mahalarta taron KILAF”24 da suka zo jihar kano domin halartar taro kan harkokin Fina-Fina suna daf da karkare taron , bayan sun kammala daukar horo Kan yadda za su inganta harkokin Fina-Fina a Africa.

Taron dai ya tara mutane daban-daban daga jihohin Nigeria da wasu kasashen Africa, in suka kwashe kimanin kwana uku,zuwa hudu suna daukar horon daga kwararrun kan harkokin Fina-Fina daban-daban.

A wannan rana ta juma’a an kewaya da mahalarta taron zuwa wuraren tarihi daban-daban dake jihar kano domin gane wa idanunsu, kayiyakin tarihin jihar Kano.

Talla

Mahalarta taron na KILAF 24 sun fara ne da ziyartar gidan Dan Hausa, inda aka kewaya da su suka ga abubun tarihi da daban-daban dake cikin gidan na Dan Hausa.

Sun kuma ziyarci gidan Sarkin Kano dake Kofar kuɗu , inda aka kewaya da su cikin gidan da wasu daga cikin fadodin dake gidan har ma da fada musu tarihin Sarakunan Kano da dai sauransu.

Haka zalika, mahalarta taron na KILAF 24 sun kuma ziyarci gidan Adana kayan tarihi na gidan Makama, Inda nan ma suka ga abubunwan tarihin Kano kala-kala.

Za mu tabbatar Yan arewa sun hukunta duk dan majalisar da ya goyi bayan tsarin harajin Tinubu – Falakin Shinkafi

Haka kuma sun ziyarci marinar Kano dake Kofar Mata da Dutsen Dala duk domin bude Ido ka kara samun ilimi.

Wasu daga cikin mahalarta taron da Kadaura24 ta zanta da su , sun bayyana jin dadinsu da wannan ziyarar, Sannan su ka ce sun sami ilimi sosai wanda zasu yi alfahari da shi.

“Babu Shakka sai yau na yarda da cewa Kano tunbin giwa ce , kuma na ga kayan tarihi ba ma na Kano ba ne kadai, tarihi ne da ya shafi duk wani bahaushe kamar tarihi Dan Hausa ka ga ai ba na yan Kano ba ne kawai na duk wani bahaushe ne”. A cewar wata Zainab Isyaku da ta zo daga sokoto

Bashir Gentile ya Gargaɗi Shugaban Majalisar Wakilai Kan Kudirin Dokar Harajin Tinubu

Wani mai suna Sulaiman Abdullahi ya ce babban abun da yafi burgeshi a Kano ne yadda aka tarbesu wanda hakan ya ce ya tabbatar masa da cewa yan Kano ba sa kyamar baki.

Taron dai kungiyar baje kolij fina-finai na harsunan Afirka wato KILAF ta shirya, wanda ya maida hankali kan janyo hankulan al’umma su rika bibiyar fina-finan da ake yi a harsunan nahiyar Afirka

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...