Hakikanin abin da ya faru dangane da cire Abdullahi T Gwarzo daga Minista – Adamu Abdullahi

Date:

Daga Adamu Abdullahi

 

Abdullahi Tijjani Gwarzo, Gogaggen ɗan siyasa tun daga tushe, , ɗan kishin kasa, jarumin da yake iya tunkarar ķalu-bale kowane iri a fagen siyasa, tsohon karamin ministan gidaje da raya birane, mutum ɗaya tilo da aka shaida a matsayin ɗan amanar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a faɗin jihar Kano tsawon shekaru.

Minista Gwarzo yana daga cikin ‘yan kaɗan a abokan siyasar Shugaba Tinubu, wadanda sukayi aiki tuƙuru na tsawon shekaru dan ganin fatansa na zama shugaban tarayyar Najeriya yacika.

Ga duk masu bibiyar al’amuran siyasa suna sane da abinda ya faru a shekarar zaɓe ta 2011, lokacin da T Gwarzo ya fice daga tsohuwar jam’iyyarsa ta ANPP bisa wani rashin adalci da akayi masa a jam’iyyar da a lokacin shi ne mataimakin gwamna, Wannan tasa ya koma jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN), wato jam’iyyar siyasar Tinubu a wancan lokaci.

Daga nan ne ya fara gina sabon tsarin siyasa, inda ya yi amfani da kwarewarsa a matsayinsa na dan siyasa tun daga tushe, Ya kuma samu damar kasancewa dan takarar gwamnan Kano a zaben 2011 daga wannan jam’iyya ta ACN.

Ba kamar yadda aka saba gani tsakanin sauran ‘yan siyasa ba, da suke iya zabar tashin hankali da batanci ga junansu yayin da aka rabu, rabuwar da T Gwarzo ya yi da Malam Ibrahim Shekarau Gwamnan Jihar Kano na wancan lokaci bai taba zama wani tashin hankali ba a siyasance, kamar yadda aka saba gani tsakanin shugabannin siyasa a Nijeriya yayinda suka saɓa. Shugabannin biyu sun rabu cikin kwanciyar hankali, mutuntawa da fahimtar juna, inda dukkansu biyun suka ci gaba da gudanar da harkokinsu na siyasa ba tare da nuna kyama ba.

Talla

Bayan ya faɗi zaɓe a shekarar 2011 Minista Gwarzo ya ci gaba da tsayawa tsayin daka a matsayin jagoran daular siyasar Tinubu a Kano dama Arewacin Najeriya. Ya cigaba da rike tutar jam’iyyar ACN har zuwa lokacin da aka narkar da ita aka koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wadda shi ne shugabanta na farko a jihar Kano.

Yayin da wasu ’yan siyasa tun daga lokacin suketa kewaye-kewaye don neman muƙami ko kwangiloli daga gwamnatin Kano dama fadar shugaban ƙasa, Minista T Gwarzo ya mayar da hankali ta karkashin kasa, yana aiki dare da rana ba tare da gajiyawa ba, domin ƙoƙarin gina katafaren gidan siyasa ga Tinubu a Kano da Arewa maso Yamma. Wanda kuma ƙoƙarinsa da ƙwazonsa, hakika, ya samu sakamako mai kyau domin burin da Shugaba Tinubu ya yi na tsayawa takarar shugabancin kasa ya samu karbuwa sosai a Kano da ma daukacin Arewa.

Abin baibada mamaki ba a lokacin da Shugaba Tinubu ya zaɓo Gwarzo a matsayin minista daga Kano. Kuma a wannan matsayi nasa na ɗan majalisar zartaswa a gwamnatin Shugaba Tinubu, Gwarzo ya yi amfani da kwarewarsa da gogewarsa a matsayinsa na tsohon shugaban shugabannin ƙananan hukumomi ALGON har karo huɗu, tsohon mataimakin gwamna kuma kwamishinan albarkatun ruwa, baya ga farin jinin Gwarzo da tsantsar ƙauna da al’umar Kano suke nuna masa saboda yadda ya share musu hawaye dangane da irin baƙar wahalar da sukesha ta rashin ruwa hakance ma tasanya suke kiransa da “Ruwa Baba” domin ya gyara hanyoyin samar da ruwan sha da dama sannan a lokacin nasa ne ya samar da sabuwar cibiyar samar da ruwan sha ta watari.

A matsayinsa na karamin minista a ma’aikatar gidaje da raya birane, Gwarzo ya samu nasarorin da ba a saba gani ba a ma’aikatar, da suka hada da aikin gina sabbin gidaje 3,112 da ake yi a Karsana Abuja; Gidaje 250 a jihohi 11 a duk shiyyoyin kasarnan; Sabbin gidaje 500 a Kano wanda a halin yanzu aikinsu ke cigaba da gudana a karkashin shirin Renewed Hope Estate and Cities. Akwai kuma shirin gina gidaje 100 a dukkan kananan hukumomin kasar nan 774 ta karkashin asusun samar da gidaje ga masu ƙaramin ƙarfi.

Minista Gwarzo, Shugaba mai tausayi da jin ƙai wanda ya saba taɓa rayuwar talakawa, tunda ya shiga ofis a duk ranar Alhamis, mabukata kan taru inda yake raba masu naira dubu biyar biyar kowannensu kuma duk yawansu da nufin taimaka musu wajen dakile matsalar tabarbarewar tattalin arziki da ke addabar al’umma. An bayyana Abdullahi Tijjani Gwarzo a matsayin mutun mai kishin jam’iyya, wanda a kodayaushe yake fifita muradan jam’iyyar sama da son ransa. A cikin sakonsa na murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai na baya-bayan nan, Minista Gwarzo ya bayyana cewa gwamnatin APC karkashin jagorancin shugaba Tinubu ta samu nasarori masu yawa da ya kamata duk ‘yan Nijeriya masu kishin kasa da masu son ci gaba su amince da su kuma su yi murna da su. Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su hada kai su yi aiki tukuru domin gina ƙasa wadda ‘ya’yanmu na gaba za su yi alfahari da ita, inda ya kara da cewa abin da Shugaba Tinubu ke bukata daga dukkan ‘yan Nijeriya shi ne goyon baya da hadin kai da zai kai kasar ga tudun mun tsira.

To sai dai kuma duk da irin rawar da mai girma tsohon ƙaramin mininta Abdullahi Tijjani Gwarzo ya bayar a fannin samar da gidaje a cikin shekara guda da shugabancinsa, da kuma irin goyon bayan da yake baiwa gwamnati, a tare da haka aka cire shi daga mukamin ministan ba tare da wani dalili ba, sai dai zargin cewa an cire shi ne saboda yadda yankin sa na Kano ta Arewa yana da dimbin manyan ‘yan siyasa da ke riƙe da manyan mukamai. Don haka aka sadaukar da muƙamin nasa zuwa ga wani yankin. Kar mu manta akwai Jihohin da suke da ministoci biyu daga karamar hukuma daya dama wadda take da guda huɗu.

Masana harkokin siyasa na kallon wannan mataki da mai girma shugaban kasa ya dauka a matsayin kashe kai a siyasance duba da matsayin Gwarzo a wurin al’ummar Kano, sannan wata maƙarƙashiya ce da wani mutum guda yake shiryawa a ƙoƙarinsa na ganin ya sharewa kansa hanya dan samun takarar gwamna a shekara ta 2027, babban kuskure ne cire ɗan siyasa mai anfani kuma mai farin jini a wajen jama’a daga muƙaminsa batare da laifin komai ba kuma a maye gurbinsa da wanda bai kama ƙafarsa ba ma ta kowwace fuska, kuma al’umar jihar Kano bazasu amince da wannan mataki ba.

Haka kuma, magoya bayan jam’iyyar APC a Kano suna kallon abubuwanda ke faruwa, sannan wannan mataki ya tayar musu da raunin da suka samu dangane da hukuncin kotun koli na gwamnan Kano, da ake zargin shi dai wancan mutum da taka rawa yanzu kuma ga maganar sauke Minista Abdullahi Tijjani Gwarzo shi ma dai wancan mutum shi ne kanwa uwar gami.

Minista Gwarzo a ɗan gajeren wa’adinsa a matsayin ƙaramin minista ya amfani ƙasa da al’umar ƙasa,, hatta ma’aikatan ma’aikatar sun tabbatar da hakan yayinda dayawansu aka hangesu suna zubda hawaye lokacin da labarin cire ministan ya riskesu, babu shakka tarihi bazai manta da irin ƙwazon aiki, sanin makama da kuma jajircewa da T Gwarzo ya nuna a wannan muƙami ba.

Wani abin sha’awa shi ne, biyayyarsa da goyon bayansa ga shugaban kasa musamman a kokarin da yake yi wajen magance kalubalen tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta da kuma kyawawan ƙudurorinsa na kishin ƙasa da ƙoƙarin ciyar da ita gaba.

Amma gaskiyar magana ita ce, an ba wa shugaban kasa shawara bisa kuskure kuma ya yanke mummunan hukunci akan amintaccen almajirinsa na siyasa.

Daga  Adamu Abdullahi

Fassara; Jabir Mukhtar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano za ta fara jiyo ra’ayoyin al’umma kafin gudanar da duk wani aiki a jihar – Bilkisu Indabo

Daga Samira Hassan   Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin nan...

Kwankwaso ya gana da Tinubu a fadar shugaban kasa

Daga Nasiba Rabi'u Yusuf   Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso,...

Neman Ilimin addini dana boko da sana’a ba kishiyoyin juna ba ne – Dr. Aminu Sagagi ga matasan Zango

Daga Rahama Umar Kwaru   Wani Malamin addinin musulunci a kano...