Zaɓen kananan hukumomi: Kotu a Kano ta sake baiwa KANSIEC sabon umarni

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Babbar kotun tarayya dake zamanta a Kano karkashin jagorancin mai Shari’a Simon Amobeda ya sake haramtawa hukumar zabe ta kasa INEC baiwa hukumar zabe ta jihar kano KANSIEC sunayen rijistocin masu zaben dake kan kowanne akwatin zabe a fadin jihar kano.

Mai Shari’a Simon Amobide ya bayyana hakan ne cikin hukuncin da ya yanke yau Juma’at a wata kara da NNPP da wani Engr. Muhd Babayo suka shigar da INEC da KANSIEC da Babban sufeton yan sandan Nigeria da Daraktan hukumar DSS .

Talla

Kadaura24 ta rawaito Alkalin kotun ya kuma ayyana Barr. Dalhatu Shehu Usman a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar NNPP reshen jihar kano, tare kuma da umartar hukumar KANSIEC da ta yi fatali da sunayen yan takarar da wani bangare da ke ikirarin shugabancin NNPP ya kawo mata muddin ba Dalhatu Shehu Usman ne.

Yanzu-yanzu: Kotu a Kano ta baiwa KANSIEC damar gudanar da zaben kananan hukumomi

Alkalin ya kuma sake dakatar da hukumar Yan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS daga sanya idanu da kuma bada tsaro a zaben da KANSIEN take shirin yi a gobe asabar.

Talla

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar talatar data gabata Babbar kotun ta ba da umarnin rushe shugabannin hukumar zaben ta KANSIEC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...