Yan Sanda a Kano sun bayyana matsayarsu kan hukuncin Kotu game da zaben kananan hukumomin

Date:

Rundunar yan Sanda ta kasa reshen jihar kano ta bayyana cewa zata mutunta umarnin babbar kotun tarayya dake kano, na cewa yan sanda su kauracewa zaɓen Kananan hukumomi jihar da aka shirya gudanarwa ranar asabar 26 ga wannan watan na October.

Talla

Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wani sakon murya da ya rabawa manema labarai.

Ya ce bayyana cewa za su bi umarni kotu da ta hana su shiga cikin tsarin tsaron zaɓen ƙananan hukumomin Jihar Kano.

Matsayar gwamnatin Kano da martanin APC Kan zaɓen Kananan hukumomi

” Kamar yadda yake a umarni na tara na hukuncin da kotun ta yanke ranar talatar, kotun ta basu umarni ba da tsaro a wurin zaben don haka zamu Mutunta umarnin da Kotu ta ba mu kuma aka kawo mana”.

Talla

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce duk da cewa ba za su shiga cikin tsarin bayar da tsaro ba a zaɓen na ranar Asabar ba, hakan ba zai hana rundunar yin sintiri don tabbatar da tsaro rayuka da dukiyoyin jama’a ba a yayin gudanar da zaɓukan a ilahirin kananan hukumomi 44 na jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...

Zargin kwace gona: Majalisar Dokokin Kano zata binciki Shugabar Karamar Hukumar Tudun Wada (ALGON)

    Majalisar dokokin jihar Kano, ta sha alwashin gudanar da...