Daga Mukhtar Yahya Shehu
Shugaban hukumar zaben jihar Kano faefesa Sani Lawal Malunfashi ya ce suna nan Kan bakansu na gudanar da zaben kananan hukumomin jihar Kano a ranar Asabar 26 ga watan oktoba na wannan shekara.

Farfesa Sani Lawal Malunfashi ya sanar da haka yayin Taron manema Labarai dangane da hukuncin babbar kotun jihar Kano na basu dama su cigaba da shirye-shiryen zaben.
Ya ce a matsayin su na masu bin doka, tun a baya kotu ta ba su dama Kuma a kan haka su ke gudanar da ayyukan hukumar.
Matsayar gwamnatin Kano da martanin APC Kan zaɓen Kananan hukumomi
” Hukuncin wannan babbar kotun jihar Kano ya bai wa hukumar zaben ta jiha damar cigaba da shirye-shiryen zaben tare Kuma da umartar duk hukumomin tsaro da ke jihar su Samar da cikakken tsaro yayin zaben.” In ji farfesa Sani Lawal Malunfashi.

” Duk da cewa ni ba lauya bane amma na san waccan jam’iyyar adawa bata da hurumim shigar da hukumar kara saboda ba ta cikin jam’iyyu 6 da suka cika sharudan hukumar na shiga zaben.” A cewar farfesa Malunfashi.
Ya ce babu APC a zaɓen ƙananan hukumomi da zai gudana a gobe Asabar.
Jam’iyyun da za su kara su ne kamar haka: AA, Accord Party, AAC, NRPM da kuma NNPP.