Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC) ta ce za a ci gaba da gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar duk da hukuncin da kotu ta yanke na korar shugabannin hukumar.
Shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya bayyana haka a wajen wani taron wayar da kan jama’a da aka yi da kungiyoyin masu Zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki kan yadda za a gudanar da zaben kananan hukumomin da ke tafe wanda kungiyar Citizen for Development and Education (CDE) tare da hadin gwiwar KANSIEC suka shirya wanda aka gudanar a Kano ranar Laraba.

Ya ce za a ci gaba da gudanar da zaben kamar yadda aka tsara, inda ya ce za su kalubalanci hukuncin a gaban wata kotun.
A zantawarsa da manema labarai babban daraktan kungiyar ta CDE Ambasada Ibrahim Waiya ya ce sun shirya taron ne domin wayar da kan al’umma kan yadda za a gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar.
Da dumi-dumi: Shugaba Tinubu ya sallami ministoci tare da maye gurbinsu da wasu
“Hakki ne da ya rataya a wuyan al’ummar Kano su fito su zabi shugabannin da suke so, kuma babu wanda ya isa ya kwace musu wannan damar don haka ya bukace su da su fito domin kada kuri’a tare da taka rawar gani sosai domin samun nasarar zaben”. Inji waiya

“Yana daga cikin tsarin zaben a wayar da kan jama’a game da yadda za a gudanar da zaben, a fada musu muhimmancin kada kuri’a a zaɓen da ka’idojin gudanar da zabe, da duk abubunwan da suka danganci zaɓen,” a cewar Waiya.
” Ko da shugaban hukumar ko babu, za a gudanar da zaben ne saboda sauran ma’aikatan KANSIEC suna nan kuma su ke da alhakin ci gaba da gudanar da aikin har a kai ga gaci ,” inji shi.

A nasa jawabin tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar wanda shi ne shugaban jami’ar Yusuf Maitama Sule ta Kano ya ce babu dimokuradiyya muddin ba za a gudanar da zabe ba, don haka ya kamata jama’a musamman na Kano su fito domin su sh zabi shugabannin kananan hukumominsu yadda ya kamata .

Al’ummar Kano da Najeriya sun daina amincewa da tsarin da ake kai, saboda suna zabi mutanen da suke so wasu kotuna kuma su canza su da wasu, mutane su zabi shugabanni amma basu ga wani chanji ba, Amma ya duk da haka akwai bukatar mutane su kara hakuri su cigaba da zabar waɗanda suke so” inji farfesa Hafiz.
“Amma duk da kalubalen da ake fuskanta, ya kamata jama’a su fito su kada kuri’a, zaben kananan hukumomi na da muhimmanci kuma kada mutane su tauyewa kansu hakkinsu,” in ji shi.