Cikakken bayani kan hukuncin da Kotu ta yi game da zaɓen kananan hukumomin Kano

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

A jiya Talatar ne wata babbar Kotun tarayya a kano ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Simon Amobeda ta rushe shugabancin hukumar zaɓe ta jahar Kano bisa dogaro da hujjojin da aka gabatar mata na rashin cancantar shugabannin hukumar bisa kasancewarsu ƴan siyasa masu ɗauke da katin Jam’iyyar NNPP.

Wani ɗan jam’iyyar APC Hon Aminu Tiga da Jam iyyarsa ta APC ne dai suka shigar da ƙara inda suka roƙi kotun da ta rushe shugabannin hukumar zaɓen ta Kano bisa kasancewrsu ƴan jam’iyya mai mulki.

Talla

Ga dai hukunce-hukuncen da kotun ta yanke:

Dukkanin Shugabannin hukumar zaɓen jihar Kano ba su cancanci jagorancin hukumar ba kasancewarsu masu ɗauke da katin jam’iyyar NNPP wanda ya ci karo da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya da aka yi wa kwaskwarima a 1999.

Shugaban hukumar zaɓen na Kano, Farfesa Sani Lawal Malumfashi bai cancanci naɗin da aka yi masa ba saboda ba ma’aikacin gwamnatin jihar Kano ba ne wanda ke ƙasa da muƙamin mataimakin darekta kamar yadda dokar hukumar zaɓen ta Kano ta 2001 ta tanada.

Gaskiyar abun da ya faru ga yan jaridar gidan gwamnatin Kano har aka sallami wasun su

Tawagar shugabannin hukumar zaɓen ta Kano ta ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya wanda aka yi wa kwaskwarima a 1999 da tanade-tanaden da suka kafa hukumar zaɓen ta Kano na 2001, saboda haka ba za su iya gudanar da zaɓe a kananan hukumomin jihar 44 ba har sai an naɗa waɗanda suka cancanta tukunna.

Duk wasu shirye-shirye da hukumar zaɓen ta yi a baya ko kuma take yi ko shirin yi a nan gaba dangane da zaɓen ƙananan hukumomi na jihar na 2024 da suka haɗa da fitar da ƙa’idojin zaɓe, tantance ƴantakara, sayar da fom ɗin shiga takara duka haramtattu ne.

Talla

Daga yanzu an rushe kuma an kori waɗanda ake ƙara daga muƙamansu na shugabancin hukumar zaɓen da mambobinta.

An hana hukumar zaɓen ta Kano gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi na 2024 har sai an naɗa waɗanda suka cancanta.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC ka da ta bai wa hukumar zaɓen ta Kano kayan zaɓe dangane da zaɓen ƙananan hukumomi na 2024 da suka haɗa da jerin sunayen masu zaɓe, har sai an naɗa waɗanda suka cancanci jan ragamar hukumar.

Talla

Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta, INEC ta yi maza ta karɓe duk wasu kayan da ta bai wa hukumar zaɓen Kano idan har ma ta yi hakan, har sai an samu shugabannin da suka cancanta a hukumar zaɓen ta Kano.

Ka da hukumar DSS ta Kano da rundunar tsaro ta NSCDC su shiga harkar zaɓen na 2024 a ƙananan hukumomi 44 na Kano har sai lokacin da aka naɗa mutanen da suka cancanta kamar yadda doka ta tanada.

Talla

Waɗanda ake ƙara na biyu (Majalisar Dokokin Kano) da na uku (Kwamishinan Shari’a na Kano) su tabbatar da cewa an bi ƙa’ida wajen naɗa mutanen da suka cancanta domin shugabancin hukumar zaɓen ta Kano kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya da aka yi wa kwaskwarima a 1999 da tanade-tanaden da suka kafa hukumar zaɓen ta Kano na 2001.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...