Shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Osun, Mista Sunday Bisi, ya gargadi Shugaban APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje, da ya guji yin furucin da zai iya tayar da tarzomar siyasa a yankin Kudu maso Yamma.
Daily Trust ta rawaito cewa Bisi, a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin, yana mayar da martani ga kalaman da Ganduje ya yi a wajen taro a Jihar Ondo, inda aka rawaito ya ce jam’iyyarsa na da dabarar “mamaye” dukkanin yankin Kudu maso Yamma.

Shugaban PDP ya gargadi Ganduje cewa irin wadannan kalaman na iya tayar da hankulan jama’a da haifar da rashin zaman lafiya a kasar.
Ya kuma jaddada cewa mutanen Osun za su yanke hukunci kan wanda zai mulke su idan lokacin ya yi.
Gaskiyar abun da ya faru ga yan jaridar gidan gwamnatin Kano har aka sallami wasun su
Yayin da yake bayyana kalaman Ganduje a matsayin “kokari na jefa yankin Kudu maso Yamma cikin rikicin siyasa da ba ya da amfani,” Bisi ya gargadi cewa Najeriya, da tuni take fama da rikice-rikicen kabilanci da kalubalen tattalin arziki, bai kamata a kara tayar mata da hankali ba.
Bisi ya ce, “Ga mutum wanda bai iya cin zabe a jiharsa ta Kano ba, saboda rashin iya mulki a wa’adinsa a matsayin gwamna, ya zo yanzu yana barazanar zuga yankin Kudu maso Yamma da wuta da hayaki ba kawai rashin hankali ba ne, amma rashin tunani ne kwata-kwata.

“Yayin da Shugaban Kasa ke ci gaba da fuskantar matsalar tattalin arzikin kasar, Ganduje ya kamata ya yi taka-tsan-tsan kada ya kara dagula lamarin ta hanyar kokarin yin magudi a zaben, musamman a yankin Kudu maso Yamma. Yin hakan zai zama tamkar taka kan maciji mai hadari.

“Idan Mallam Ganduje ya kasa, kamar yadda ya yi, wajen tayar da rikici a Kano, inda aka yi watsi da APC saboda mulkinsa mai tsanani, ya kamata ya shirya karbar irin wannan sakamakon a wasu jihohin da APC ta kasa gamsar da masu zabe.”