Iftila’i: Yan wasan Kano Pillars sun yi haɗari a Jos

Date:

 

Tawagar kungiyar kwallon kafa ta ‘yan kasa da shekaru 19 na Kano Pillars ta yi haɗari a garin Jos.

Tawagar ta yi haɗarin ne a hanyarsu ta zuwa filin wasa na Jos domin buga wasa a gasar matasa ta ‘yan kasa da shekaru 19.

Talla

Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da sashin yada labarai na kungiyar ya fitar a yau Talata.

“Muna bakincin sanar da cewa, motar da ke dauke da tawagar U-19 ta Kano Pillars FC ta yi hatsarin mota a yau, yayin da take kan hanyarta zuwa Sabon Filin Wasa na Jos don buga wasan cikon mako na 5 a gasar matasa ta U-19 da Plateau United .

Talla

“Wasu daga cikin ‘yan wasan da direban sun ji rauni a wannan mummunan al’amari, kuma an gaggauta kai su asibiti don samun kulawar likitoci. Alhamdulillahi, ba a samu asarar rai ba a wannan lokaci, kuma tawagar likitocin na ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...