Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben da ya gabata Peter Obi, ya bayyana fashewar tankar mai da ta afku a Majiya dake jihar jigawa wanda ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 180 a matsayin wani babban Iftila’i da ya shafi al’ummar kasar baki daya.
Peter Obi ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar jajewa gwamnati da al’ummar jihar Jigawa a Dutse bisa faruwar wannan lamari na bakin ciki .

Ya shawarci gwamnati a dukkan matakai da su kara kaimi wajen samar da duk wasu hanyoyin da za su tabbatar da kare rayukan ‘yan Najeriya.
Dan takarar shugaban kasar ya yi kira ga Direbobin motocin dakon mai da su rika yin taka-tsan-tsan yayin da suka dauko mai, inda ya bukace su da su tabbatar da duk matakan da suka dace da nufin dakile sake afkuwar irin wannan abin bakin ciki a nan gaba.
Peter Obi ya yabawa gwamnati da al’ummar jihar Jigawa bisa matakan da aka dauka tallafa wa iyalan wadanda abin ya shafa.

A jawabinsa Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi ya yaba da ’yan uwantakar da Peter Obi ya nuna ta hanyar sadaukar da lokacinsa don zuwa jihar domin ya jajanta musu bisa Iftila’in da ya faru.
“Ziyarar ku ta nuni da cewa mu yan Nigeriya uwa daya uba daya muke, kuma ta nuna yadda ka damu da rayuwar dukkan ‘yan Najeriya”.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar jigawa ta dauki matakin gaggawa tun bayan faruwar lamarin da nufin tallafawa iyalan wadanda abin ya shafa .
Ya kuma yaba da damuwar da daukacin al’ummar Nigeriya suka nuna kan bala’in da ya shafi jihar jigawa.