Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci kimanin yan jarida 14 da ake aiki a Ofishin gwamnan jihar kano da su koma kafafen yada labaransu ba sa bukatar cigaba da aiki da su.
A zantawar da jaridar KADAURA24 ta yi da wasu cikin yan jaridar da abun ya shafa bisa sharadin sakaye Sunansu, sun bayyana mana ce duk da cewa gwamnatin ba ta fadi wani dalili na Neman janye su ba, Amma suna ganin batun ba zai rasa nasaba da wasu abubuwa guda biyu da suka faru a makon da ya gabata ba.

Na Farko akwai batun zuwan gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad Kano, na biyu kuma ziyarar da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya kai jihar Jigawa domin jajantawa wadanda gobarar tankar mai ta shafa a jihar.
“Muna zaune Darakta wayar da kan al’umma na gidan gwamnati ya ba mu umarnin mu taso mu je domin ganawa da gwamnan Kasancewar gwamnan shi ne uban wata kungiyar da shi daraktan yake jagoranta a nan jihar Kano”.
Gobarar mai a Jigawa: Peter Obi Ya Jajantawa Gwamnati, Iyalan Wadanda Suka Rasu
Ya ce bayan sun Isa Otel din da gwamnan na Bauchi ya sauka sun nemi ganawa da shi, amma cikin hadiman gwamnan wani ya ce musu su jira gwamnan ya je wata unguwa ya dawo in ya so sai su gana da shi.
“Bayan Mun jira shi ya dawo wasu daga cikin mu sun shiga domin yin ganin, sai na hangi guda cikin ‘ya’yan gwamnan Kano, amma gaskiya ban san sunansa ba, kawai sai na ga ya fito daga cikin Otel din yana wasa Ashe wai COS ya kirawo ya sanar da shi zuwanmu”.

Ya ce basu sami ganawa da gwamnan jihar Bauchin ba saboda wasu uzurori da suka taso masa, haka muka koma Ofis, “Kwatsam muna zaune sai aka ce kwamishinan yada labarai na Kano ya aiko wai a bashi sunayen wadanda suka je suka gana da gwamnan Bauchi domin ya yo mana aike hakan tasa muka hada sunayen mu mu 14 suna tura masa”.
” Jiya muna zaune sai kawai sai ga mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya Sanya wani sako da yake cewa an Bashir umarnin ya bukace mu mu koma kafafen yada labaranmu sun gode ba sa bukatar cigaba da aiki da mu”
Ya rubuta: “Masu ‘yan jarida,” in ji shi, “Ku ba ni izini in gode muku bisa aikin da muka yi da ku tsahon shekara ɗaya da ƴan watanni da suka gabata. Abin takaici, yayin da na Yi tafiya Jamhuriyar Serbia a makon da ya gabata, wasu batutuwa sun faru kuma shugabanni sun yanke shawara a wannan mawuyacin lokaci.”
Sanarwar ta fitar da sunayen ‘yan jarida 14 da abin ya shafa, da suka hadar da:- Aliyu Yusuf, Daraktan wayar da kan jama’a- Sani Suraj Abubakar, PRO- Adamu Dabo, Chairman Press Crew – FRCN- Naziru Yau, ARTV- Sadiq Sani AA, ARTV- Rabiu Sunusi, Triumph- Umar Sheka, Freedom- Jabir Dan ‘abba, Nasara- Labaran Sound- Simon, AIT Cameraman- Nasiru Danhaki, NTA- Abdullahi Sule, Driver- Murtala Baba Kusa, Express- Ibrahim Muazzam, Radio Kano.

Dalili ba biyu Majiyoyin kadaura24 suka ce shi ne abun da ya faru yayin ziyarar jajantawa da Gwamna Yusuf ya kai jihar Jigawa sakamakon fashewar tankar mai.
Rikicin da ya barke tsakanin ‘yan jarida na gidan gwamnatin Kano da jami’an DSS a gidan gwamnatin Jigawa kan hana su shiga Ofishin gwamnan wanda hakan ya janyo cece-kuce.
Ya ce waɗannan su ne dalili da suke ganin su ne suka sa aka dauki matakin akansu, Amma dai ya ce sun fi karfafa batun zuwansu wajen gwamnan jihar Bauchi.