Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa kafa jami’ar Northwest da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano dake Wudil sune manyan nasarorin da ya samu a tsawon wa’adi zango biyu da ya yi yana mulkin jihar.
Kwankwaso, wanda shi ne jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, ya bayyana haka, a wajen Bikin kaddamar da wani shirin horas da malamai da nufin bunkasa ilimin na’ura mai kwakwalwa wato kwamfuta ga malaman firamare da sakandare guda 1,000, wanda zai kasance tare da hadin gwiwar jami’ar Skyline ta Najeriya da ke Kano a ranar Litinin.
Taron dai na daga cikin bukukuwan cikarsa shekaru 68 da haihuwa.

A cewar Kwankwaso, a tsahon shekaru takwas da ya yi yana gwamanan Kano, ya yi ayyukan raya kasa da dama da suka hada da bunkasa noma, samar da ababen more rayuwa, da raya karkara, da dai sauransu amma ya fi alfahari da kafa jami’o’in guda biyu .
Kwankwaso ya kuma yabawa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf bisa jajircewarsa na bunkasa harkokin ilimi a jihar.
Dr. Saleh Musa Wailare ya taya Kwankwaso murnar cika shekaru 68
A cewar Kwankwaso, Gwamna Yusuf ya cancanci yabo domin har yanzu yana tafiya akan akidar Kwankwasiyya, da ta kunshi bunkasa ilimi da ci gaban dan Adam.
A nasa jawabin, gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya yaba da shirin horar da malamai 1,000 kan ilimin kwamfuta tare da hadin gwiwar jami’ar mai zaman kanta.
Gwamna Abba ya taya Kwankwaso cika shekaru 68 a duniya
Yusuf ya kara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da hada kai da jami’o’i masu zaman kansu wajen horar da malamai da kuma kara kwazo domin samun nagartar ilimi a jihar.
Ya yabawa Kwankwaso a matsayin jagoransa, ya kuma yi alkawarin ci gaba da tafiya a kan turbar Kwankwasiyya.
A nasa jawabin tun da farko, kodinetan shirin kuma kwamishinan ilimi mai zurfi, Dakta Yusuf Ibrahim Kofar-Mata, ya ce shirin ya zo ne a daidai lokacin da ilimi, fasaha, da kere-kere su ne ginshikin ci gaban kowace al’umma.

“A yau mun kaddamar da shirin horar da malamai da nufin inganta ilimin kwamfuta na malaman makarantun Firamare da Sakandare 1,000, kuma mun kaddamar da ba su satifiket ga wadanda suka cancanta, sannan mun kaddamar da shirin bunkasa rayuwar matasa maza da mata kimanin 100 Kan harkokin fasaha da kirkira”.
“Wannan gagarumin aiki, wanda aka aiwatar tare da haɗin gwiwar Jami’ar Skyline, ya zo ne a lokacin da ilimi, fasaha, da kirkire-kirkire ke haifar da gagarumin ci gaba ga kowace al’umma. Wadannan tsare-tsare za su ƙarfafawa kwarewar malamanmu ta yadda za su baiwa ya’yanmu Ilimin mai inganci.

Bayan kammala taron, Kwankwaso ya zarce zuwa Rikadawa, karamar hukumar Madobi, mahaifarsa, inda ya bude makarantar firamare ta Islamiyya, a wani bangare na bikin cikarsa shekaru 68 a duniya.
Bayan duba sabuwar makarantar da aka gina, Kwankwaso ya bayyana jin dadinsa da aikin, wanda a cewarsa, zai taimaka matuka wajen taimakawa al’umma wajen kara samun ilimin addinin musulunci.