Jam’iyyar NNPP ta dakatar da sakataren gwamnatin jihar Kano, Dakta Abdullahi Baffa Bichi, da kwamishinan sufuri, Muhammad Diggol daga jam’iyyar.
Shugaban jam’iyyar na jihar Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa ne ya sanar da hakan a yammacin ranar Litinin.
A cewar Dungurawa, dakatarwar ta biyo bayan korafe-korafensu da ake kaiwa shugabannin mazabunisu da na kananan hukumomi na jam’iyyar.
Dungurawa ya ce an dakatar da su ne saboda rashin mutunta jam’iyyar da shugabancinta.
Tinubu ya buƙaci CAF ta ɗauki mataki kan Libya
“Jam’iyyar ba za ta lamunci duk wani abu na raina shugabancinta da tsarinta ba. Bayan da muka samu wasikun korafe-korafe daga al’umma, sannan kuma muka tabbatar da zargin ta hannun shugabannin kananan hukumomin su, ba mu da wani zabi illa daukar wannan muhimmin mataki,” in ji Dungurawa.
Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano ta Arewa a karkashin jagorancin Sulaiman Dambatta, ya kara tabbatar da wannan zargi, wanda ya kai ga yanke hukuncin dakatar da jami’an guda biyu.
Idan za a iya tunawa a yan Kwanakin nan ana ta zargin Sakataren gwamnatin Kano Dr. Baffa Bichi bisa daukar nauyin wata kungiya mai suna ” Abba tsaya da kararka” wacce take rajin ganin an sami farraku tsakanin Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da jagoran jam’iyyar NNPP na kasa Rabi’u Musa Kwankwaso.
Solacebase