Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Doguwa/Tudunwada, Alhassan Ado Doguwa, ya mayar da martani kan furucin da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi cewa ’yan Najeriya za su kayar da jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Kwankwaso, a lokacin da yake jawabi a wani taron siyasa a Kano, ya ce ’yan Najeriya, musamman ma ’yan Arewa, sun gaji da APC kuma za su sauya ta a zaɓen 2027.

Doguwa, ya ce Kwankwaso har yanzu bai farfaɗo daga kayen da ya sha a hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2023 ba.
Ya shawarci Kwankwaso ya daina mafarki ya fara neman mafita game da siyasarsa kafin zaɓen 2027.
“A bayyana yake cewar Kwankwaso bai gama warkewa daga shan kaye da ya yi a 2023 a hannun Shugaba Tinubu ba. Furucinsa na cewa ‘yan Najeriya sun gaji da APC ba komai ba ne face mafarki. Ya kamata ya nemi mafita kafin zaɓen 2027,” in ji Doguwa.
Tsohon hadimin Buhari a Kano ya kalubalanci kalaman Kwankwaso akan Peter Obi
Doguwa, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Albarkatun Man Fetur, ya ce kalaman Kwankwaso ba su da ma’ana.
“A wani taron siyasa, Kwankwaso ya yi iƙirarin cewa za a sauya APC a 2027. Lokaci ya yi da zai daina mafarki kuma ya amince cewa lokacinsa a siyasa yana gab da ƙarewa.”

Doguwa ya ƙara da cewa Tinubu yana aiki tuƙuru wajen gyara tattalin arzikin ƙasar da inganta al’amura.
Doguwa ya bayyana cewa ya na da yaƙinin cewa matsalolin da ake fuskanta a ƙasar za su ragu nan ba da jimawa ba, yayin da matakan da shugaban ƙasa ya ɗauka za su fara bayar da sakamako mai kyau.