Ranar Malamai 2024: NUT ta karrama Gwamnan Kano bisa kawo sauyi a fannin ilimi

Date:

Kungiyar malamai ta Najeriya (NUT) ta karrama gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, da lambar yabo ta musamman saboda kwazon da ya nuna wajen gyara fannin ilimi a jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya aikowa kadaura24 a ranar Asabar.

Kungiyar ta baiwa gwamnan kyautar ne a yayin bikin ranar malamai ta duniya ta 2024 a dandalin Eagle Square da ke Abuja, a wani gagarumin taron da aka shirya tare da hadin gwiwar ma’aikatar ilimi ta tarayya.

Taron ya tattaro malamai daga jahohi 36 na Najeriya domin karrama wadanda suka ba da gagarumar gudunmawar a fannin ilimi.

An karrama Gwamna Yusuf da lambar yabo ta NUT Golden Award saboda kokarin da ya yi wajen ganin an ceto fannin ilimi na Kano daga rugujewar saboda rashin kulawa.

Tsohon hadimin Buhari a Kano ya kalubalanci kalaman Kwankwaso akan Peter Obi

A nasa jawabin, shugaban NUT na kasa, Kwamared Titus Ambe, ya bayyana cewa gwamnoni shida ne kawai aka zaba domin karramawa, bisa jajircewarsu wajen a ci gaban ilimi, musamman ta hanyar tallafa wa jin dadin malamai da ci gaba da horar da su.

Yayin taron an bayyana nasarorin da Gwamna Yusuf ya samu, ciki har da yadda gwamnatinsa ta ware kashi 29.9 na kasafin kudin Kano na 2024 ga ilimi da kuma ayyana dokar ta-baci a fannin, wanda ya inganta dukkanin ababen more rayuwa da samar da ingantaccen ilimi a jihar.

Talla

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wanda sakataren gwamnatin tarayya Sanata George Akume ya wakilta ya yabawa gwamnonin bisa sadaukarwar da suka yi.

Da yake jawabi a madadin wadanda aka karrama guda shida da suka hada da Gwamnonin jihohin Borno, Oyo, Benue, Enugu, da Kebbi, Gwamna Yusuf ya jaddada kudirinsa na kara saka hannun jari a fannin ilimi, domin cigaban al’umma .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...