Za mu baiwa MD ARTV haɗin kai don ta sami nasarar da Kanawa za su yi alfahari da ita – RATTAWU

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Kungiyar ma’aikatan radio da talabijin ta kasa reshen jihar kano RATTAWU ta ba da tabbacin baiwa shugabar gidan talabijin ta ARTV Hajiya Hauwa Isa Ibrahim haɗin kan da ya dace domin ciyar da gidan talabijin din gaba.

” A shirye muke mu ba ki duk wani hadin kai da kike bukata domin inganta aiyukan wannan gidan talabijin mai tarihi Kano, wanda duk dan jihar kano da Arewacin Nigeria ke alfahari da shi”.

Talla

Shugaban kungiyar na jihar kano Kwamaret Babangida Mamuda Biyamusu ne ya bayyana hakan lokacin da suka ziyarci gidan talabijin din domin taya Hajiya Hauwa Isa Ibrahim murnar tabbatar da ita da gwamnan Kano yayi akan kujerar Shugabancin gidan.

Mutane 7 sun rasu sakamakon Cutar kwalara a Kano

” Ya Zama wajibi mu zo kafa-kafa domin mu taya ki murnar wannan gagarumin cigaba na tabbatar miki da wannan kujera ta MD ARTV, babu shakka gwamna ya ajiye kurya a gurbinta”. Inji Kwamaret Babangida

Ya ce tun lokacin da Hajiya Hauwa take rikon kwaryar kujerar MD ARTV ta himmatu wajen dawo da martabar gidan talabijin din da kuma samar da kayan aiki na zamani a tashar. Don haka muna godewa gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa wannan abun alkhairin da yayi”.

Talla

Da take nata jawabin shugaban gidan talabijin din ta ARTV Hajiya Hauwa Isa Ibrahim ta nuna farin cikinta bisa yadda kungiyar RATTAWU ta ta taya ta murnar tabbatar da ita akan kujerar shugaban gidan talabijin ta ARTV.

” Na ji dadi sosai kuma Ina nema hadin kan kungiyar RATTAWU ta bani hadin kai don na sami nasara yadda ake bukata ta yadda zan yi aiyukan da gwamna da al’ummar jihar Kano za su yi alfahari da ni”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...