Daga Sani Idris Maiwaya
Sama da mambobin jam’iyyar APC 960, karkashin jagorancin Alhaji Baba Sabiu, shugaban jam’iyyar a karamar hukumar Dala, sukw sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP.
Wannan sauya shekar na zuwa ne gabanin zaben kananan hukumomi da za a gudanar a ranar 26 ga watan Oktoba mai zuwa.
Wadanda suka sauya sheka da suka hada da tsaffin kansilolin mazabu 12 na karamar hukumar Dala, sun bayyana cewa suna bukatar ci gaba shi yasa suka koma jam’iyyar NNPP.

Alhaji Sabiu, a madadin sauran masu sauya shekar, ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwar jam’iyyar NNPP za ta iya kawo sauye-sauye masu ma’ana, wadanda za su iya bata damar zashe duk wani da zabe da za’a yi nan gaba.
Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi wa sabbin ‘yan jam’iyyar barka da zuwa, inda ya tabbatar musu da cewa da su da wadanda suka dade a jam’iyyar duk daya suke.
Ya nanata kudurin jam’iyyar NNPP na bunkasa zamantakewa da tattalin arziki da siyasa a Najeriya, tare da mai da hankali sosai kan ajandar 2027.

“NNPP ta himmatu wajen inganta hadin kai da kuma ciyar da Nijeriya gaba,” in ji Kwankwaso, inda ya bukaci mazauna Kano da ‘yan Nijeriya baki daya da su marawa ‘yan takarar jam’iyyar baya a zabe mai zuwa.
Ya kuma yi kira ga yan Nigeria da su fito baki daya su marawa jam’iyyar NNPP baya, tare da jaddada manufar jam’iyyar na samar da dunkulalliyar Nijeriya.