Jam’iyyar NNPP ta sauya wanda zai yi mata takarar Shugabancin Ƙaramar Hukumar Kumbotso a zaɓen Ƙananan Hukumomi mai zuwa.

Wata majiya a jam’iyyar ta tabbatar wa Freedom Radio cewa an sauya Ali Musa Hard Worker da Ghali Abdullahi Basaaf saboda wasu dalilai.
Kotu ta sanya ranar cigaba da Shari’a tsakanin Gwamnatin Kano da Sarki Aminu Ado Bayero
Ghali Basaaf tsohon Shugaban Ƙungiyar Kwankwasiyya Reporters ne na ƙasa kafin daga bisani Gwamnan Kano ya naɗa shi a maitaimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa za a gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomin jihar kano a ranar 26 ga watan October nan da muke ciki.