Daga Isa Ahmad Getso
Majalisar wakilan Najeriya ta sa kafa ta rushe lambar girman da shugaban kasa Bola Tinubu ya bai wa shugaban ta Tajudeen Abbas na CFR.

‘Yan majalisar suka bayyana fusatarsu da ba shi lambar wanda suka bayyana ta a matsayin bata dace da girman kujerarsa ba, inda suka bukaci sauya masa da irin wadda aka bai wa shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ta GCON da kuma babban mai shari’a ta kasa.
Da dumi-dumi: Tinubu zai tafi hutu Burtaniya
Majalisar ta ce babu ban-banci tsakanin Akpabio da Abbas, saboda haka ya dace a bai wa shugaban su irin lambar da aka bai wa Akpabio ta GCON maimakon CFR.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito shugaban ƙasa Bola Tinubu ya baiwa wasu mutane lambobin girmamawa na kasa, inda ya baiwa shugaban majalisar wakilai lambar yabo ta CFR, a jawabin da ya yiwa yan Nigeria a ranar cikar kasar Shekaru 64 da samun yancin kai.