Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya mika sunayen mambobin hukumar gudanarwa na hukumar raya yankin Arewa maso yamma (NWDC) ga majalisar dattawa domin tantancewa.
A cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru Bayo Onanuga ya fitar, ya ce matakin ya biyo bayan rattaba hannun da shugaba Tinubu ya yi na kafa dokar hukumar raya yankin arewa maso yamma a ranar 24 ga watan Yuli, wanda ke nuna muhimmin aiwatar da dokar hukumar.
A cewar sanarwar Ambasada Haruna Ginsau daga Jigawa shi ne zai shugaban hukumar gudanarwar hakumar
Farfesa Abdullahi Shehu Ma’aji (Kano) kuma shi ne shugaban hukumar
Yayin da Membobin suka hada da Dr. Yahaya Umar Namahe (Sokoto),
Hon. Aminu Suleiman (Kebbi)
Sen. Tijjani Yahaya Kaura (Zamfara)
Hon. Abdulkadir S. Usman (Kaduna)
Hon. Engr. Muhammad Ali Wudil (Kano)
Shamsu Sule (Katsina) da Nasidi Ali mai wakiltar jihar Jigawa.
Ana sa ran ‘yan kwamitin da aka nada za su ba da gudummawa tare da nuna ƙwarewa wajen ciyar da hukumar bunkasa yankin Arewa maso Yamma.
Hukumar ta NWDC za ta mayar da hankali wajen samar da gagarumin ci gaba, ta fuskar tattalin arziki, da zamantakewa a yankin Arewa maso yammacin Nigeria