Daga Sani Idris Maiwaya
Dr. Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya jajantawa iyalan jami’an ‘yan sanda biyar da suka mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su yayin da suke dawowa Kano daga jihar Edo.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a makon da ya gabata ne yan Sandan suka yi tsarin yayin da suke hayarsu ta dawowa Kano daga jihar Edo bayan kammala aikin ba da tsaro da suka yi yayin zaɓen gwamnan jihar ta Edo.
Ganduje ya yi wannan bayyanin ne a babban masallacin Bichi, yayin da yake mika ta’aziyya da addu’o’i ga jami’an ‘yan sandan da suka rasu.
Ya bayyana lamarin a matsayin wani abin bakin ciki ga rundunar ‘yan sanda, da shi kansa, da kuma kasa baki daya.
Tinubu ya nada dan Kano a matsayin shugaban hukumar bunkasa arewa maso yammaci
Jam’iyyar ta bayar da gudummawar Naira miliyan 2 ga iyalan duk jami’an sanya biyar din da suka rasu.
Sannan ta ba da kyautar Naira miliyan daya ga jami’an yan sanda goma da suka jikkata.
“Ni da kaina na yanke shawarar zuwa kafa-kafa har Bichi don in mika ta’aziyya ta ga iyalan jami’an ‘yan sandan da suka rasu a bakin aiki.
Shi ma shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar Abubakar Kabir Abubakar, ya mika ta’aziyyarsa, tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.