An kori wani ɗan siyasa daga gidansa bayan da matarsa ta jinginar da shi ta ciyo bashi

Date:

An kori tsohon dan takarar Gwamnan jihar Benue na jam’iyyar ACC, Ewaoche Benjamin Obe daga gidansa bayan matar sa ta bada jinginar gidan don karbo bashi.

DAILY POST ta rawaito cewa gidan yana unguwar Sagwari Layout a karamar hukumar Bwari ta birnin tarayya Abuja.

Talla

Matar mai suna Christiana Obe ta auri Obe ne tun shekarar 2006. Ma’auratan sun fito ne daga karamar hukumar Ogbadibo ta jihar Benue.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba 25 ga watan Satumba na 2025.

Na Fara Cimma Burina na Farfado da Martabar Gidan Rediyon Jihar Kano – Abubakar Adamu Rano

Obe, wanda ke kan hanyar sa ta zuwa Benue ya samu kiran waya cewa wasu jami’an tsaron sun dira a gidansa kuma sun fara shirin korar sa daga gidan.

Jin bacin rai kan lamarin, dan siyasar ya juya akalar motarsa zuwa gidan nasa.

Talla

Sai dai zuwan sa ke da wuya aka nuna masa takardun kotu dake nuni da cewa an karbe gidan nasa sakamon bashin da ake bin matar sa.

Sai dai yayin da ak la tuntubi matar tasa, sai ta kada baki ta ce “Ba dole ne sai na yi magana da kowa ba”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zaizayar kasa: Gwamna Abba gida-gida ya raba diyyar Naira Miliyan 600 A Kano

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Dalilin da ya hana Sarki Aminu Ado Bayero zuwa gidan yari na goron dutse a yau alhamis

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Rahotanni sun tabbatar da cewa Sarkin...

Matakai 3 da gwamnatin Kano ta dauka kan kafafen yada labarai a jihar

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnatin jihar Kano ta ce a...

Yadda manoma a Kano suka zargi jami’an Civil defense da karbar kudade a wajensu

Daga Umar Ibrahim kyarana   Manoman dajin dansoshiya dake karamar hukumar...