Gwamnatin Bauchi ta kammala gina gidaje 2000 domin rabawa al’umma – Kwamishinan Muhalli da Gidaje

Date:

Daga Abubakar Yakubu

 

Kwamishinan ma’aikatar gidaje da muhalli na jihar Bauchi Hon. Danlami Ahmad Kawule ya bayyana cewa gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamnan jihar Sanata Bala Muhammad ta kammala gina gidaje kimanin guda 2000 domin rabawa ga al’ummar jihar.

” A kokarinsa na ganin ya saukakawa al’ummar jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad kauran Bauchi ya gina gidaje 2000 wadanda za a raba su ga rukunonin al’umma daban-daban a jihar ta Bauchi”. Inji Hon. Kawule

Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da jaridar kadaura24 a Kano.

Talla

Ya ce saboda hangen nesan gwamnan ya ce za a raba gidajen ne ga ma’aikatan gwamnatin da masu bukata ta musamman da Mata da matasan jihar ba tare da la’akari da bambanci jam’iyya ba.

” An samar da gidajen a masarautar Ningi da Misau da Katagun da masarautar Bauchi don ganin kowanne bangare ya sami gidaje yadda aka tsara a farashi mai saukin gaske”. A cewar Kawule

Sanya Haraji mai yawa akan taba sigari ne kadai hanyar magance shan ta – CISLAC

Da yake magana kan batun muhalli a wajen wani taro na masu ruwa da tsaki kan yadda za a samar da dokokin da zasu taimaka wajen magance shan taba sigari, Hon. Danlami Kawule ya ce tuni gwamnatin jihar Bauchi ta yi nisa wajen ganin ta samar da duk dokokin da zasu inganta muhalli a jihar.

Talla

” Mun hada kai da ma’aikatar muhalli ta kasa domin wayar da kan yara yan firamare muhimmancin tashen itatuwa domin su taso da dabi’ar don magance matsalolin dumamar yanayi a jihar, Sannan tuni mun fara aikin dashen itatuwa a lungu da sako na jihar Bauchi”.

Danlami Kawule wanda shi ne Barden Arewan Bauchi ya ba da tabbacin zasu cigaba da yin duk mai yiwuwa wajen ganin sun dauki matakan da zasu magance matsalolin dumamar yanayi da yake addabar al’ummar duniya a yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...