Takutaha: Mu dage da addu’ar neman sauki a wajen Allah kan halin da Nigeria take ciki – Falakin Shinkafi ga Musulmi

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Amb. (Dr). Yunusa Yusuf Hamza Falakin Shinkafi ya bukaci al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan rana ta takutaha wajen yin addu’o’in neman Allah ya fitar da Nigeria daga mawuyacin halin da take ciki .

” Wannan rana ce mai tarin Albarka a wajen mu, don haka akwai bukatar mu tsaya mu ribaci ranar ta hanyar yiwa Annabi Muhammad Sallahu alaihi wasallam Salati, da yin Karatun al’qur’ani da sadaka tare da yin tawassali da su a wajen Allah don ya yaye mana halin kuncin da muke ciki a Nigeria”.

Falakin Shinkafi ya bayyana hakan ne cikin wani sakon taya al’ummar Musulmi Murnar zagayowar ranar takutaha ta bana, Wanda ya aikowa kadaura24.

Masana sun fara sukar matakin gwamnatin Kano na soke jami’ar ilimi ta Sa’adatu Rimi

Ya ce Nigeria ta na cikin mawuyacin halin da ya kamata al’ummar kasar su koma ga Allah domin neman sauƙi a wajen Allah, domin shi yake jarabtar bayinsa kuma shi ne yake yaye musu.

Falakin Shinkafi wanda kuma shi ne Jarman Matasan Arewacin Nigeria, ya ce addu’a ce kadai zata sauyawa yan Nigeria halin da suke ciki, kuma ya ce akwai yakinin idan aka yi addu’a a wannan rana Allah zai karba saboda rana ce da ake nunawa wanda yafi so kauna.

Talla

Ya kuma yi kira ga shugabanni a dukkanin matakai da su fito da tsare-tsare wadanda za su saukakawa al’umma, saboda mawuyacin halin da yan Nigeria suke ciki a wannan lokaci.

Amb. Dr. Yunusa Yusuf Hamza ya ce yana taya daukacin al’ummar Musulmin Nigeria da duniya baki daya murnar zagayowar watan da aka haifi fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallahu alaihi wasallam.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano za ta fara jiyo ra’ayoyin al’umma kafin gudanar da duk wani aiki a jihar – Bilkisu Indabo

Daga Samira Hassan   Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin nan...

Kwankwaso ya gana da Tinubu a fadar shugaban kasa

Daga Nasiba Rabi'u Yusuf   Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso,...

Neman Ilimin addini dana boko da sana’a ba kishiyoyin juna ba ne – Dr. Aminu Sagagi ga matasan Zango

Daga Rahama Umar Kwaru   Wani Malamin addinin musulunci a kano...