Hanya ɗaya tak da za a inganta rayuwar yaran da ke barace-barace a Kano da Arewa — Daga Mustapha Hodi Adamu

Date:

Ra’ayin Mustapha Hodi Adamu

 

Wani Dan jarida a Kano ya bayyana cewa yana ganin da gwamnatin Kano za ta haɗa kai da Alhaji Aliko Dangote, Alhaji Aminu Dantata da Alhaji Abdussamad Isyaku Rabi’u, a gina katafarun makarantun kwana na firamare da sakandire don yaran nan maza da mata da ke barace-barace a kwararo-kwararo a cikin birnin Kano, da an samu ci gaba wajen ilimi da zaman lafiya a jihar.

In har Dangote da Dantata za su iya bada gudummawar Naira biliyan 1.5 kowannen su a wata jiha da ba tasu ba, to kuwa idan aka tuntube su akan wannan gagarumin aiki, tabbas ina da yaƙinin za su bada gudunmawa mai gwaɓi.

Yawaitar ƙananan yara da ke barace-barace a unguwanni da tituna a jihar Kano ya damu kowa kuma ya sanya fargabar illar hakan a nan gaba. Waɗannan yaran barazana ne ga jihar Kano da ma Arewa baki daya.

Takutaha: Mu dage da addu’ar neman sauki a wajen Allah kan halin da Nigeria take ciki – Falakin Shinkafi ga Musulmi

Amma idan aka kwashe su, aka kai su makarantun, aka rika koya musu karatu da sana’o’i a lokacin da su ke karatun to za a taimaka wa rayuwar su kuma su ma za su taimakawa al’umma.

In ba haka ba, da wasa da wasa za su zamo wa jihar gagarumar matsala (Allah Ya kiyaye).

Idan gwamnati ta tuntubi waɗannan attajirai da na lissafo a sama, ta kuma haɗa da ƴan siyasar mu da su ka shahara a fannin mulki kamar irin su tsofaffin gwamnonin Kano – Mal. Ibrahim Shekarau, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso da Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Talla

Sai kuma masu ci a yanzu irin su Sanata Barau Jibrin, Sanata Kawu Sumaila, Sanata Rufai Sani Hanga da sauran ƴan siyasa da masu hannu da shuni, akan su bada gudunmawa wajen gina waɗannan makarantu, in sha Allahu za su taimaka.

Haka zalika idan an tashi gina makarantun, sai a gina su a shiyyoyi uku na Kano – Kano ta Tsakiya, Kano ta Arewa da Kano ta Kudu, sannan a fitar da tsari mai kyau da zai ɗorar da zaman waɗannan makarantu har illa ma sha Allah.

Khalifa Dankadai kadai idan aka bashi project din nan zai yi delivering sosai domin ya san kan harkar empowering almajirai.

Allah Ya sa gwamnati ta ji ta kuma dauki wannan shawara ta wa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta yanke wa wani hukuncin daurin gidan yari bisa laifin kona tayoyin mota a Kano

Ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi ta jihar Kano ta...

Bayan ficewa daga PDP Dino Melaye ya koma ADC

Tsohon ɗan jamalisar dattawan Najeriya mai wakiltar Kogi ta...

Ƴan Ghana na zanga-zangar neman korar ƴan Nijeriya daga ƙasar

  Zanga-zanga ta ɓarke a Ghana inda ake zargin ƴan...

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...