Tinubu ya fi ƙarfin satar dukiyar Najeriya — Minista

Date:

 

Ƙaramin Ministan Harkokin Matasa, Ayodele Olawande, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya fi ƙarfin ya saci dukiyar Najeriya.

Da yake jawabi a wajen taron Ƙungiyar Haɗin Kan Ma’aikata (JUNC), a Ma’aikatar Harkokin Ci Gaban Matasa a Abuja, Olawande, ya yi kira ga ‘yan Najeriya su ƙara haƙuri da halin da ake ciki a ƙasar nan.

Ya yi alƙawarin cewa nan ba da daɗewa ba za a ga sauye-sauyen da suka dace.

Dalori ya taya al’ummar Musulmi Murnar Bikin Mauludin Annabi S A W

Ya bayyana cewa Tinubu mutum ne mai arziƙi, kuma ba shi da sha’awar satar dukiyar ƙasar nan.“Tinubu ba talaka ba ne; ya jima da samun arziƙi, don haka ba shi da sha’awar satar dukiyar Najeriya,” in ji Olawande.

Ya kuma bayyana cewa shugabanci ba abu ne da zak dauwama ba, abin da ya fi muhimmanci shi ne irin gudunmawar da shugabanni suka bayar a lokacin da suke kan mulki.

Maulidi: Minista T Gwarzo ya bukaci al’ummar Musulmi su rika koyi da halayen Annabi S A W

Tinubu wanda ya yi gwamna har sau biyu kuma ya taɓa zama Sanata, yana da hannun jari da yawa a wurare da suka haɗa da gidaje, aikin jarida, da harkar shaƙatawa.

A wani taro kafin rantsar da Tinubu, uwargidansa, Oluremi Tinubu, ta ce iyalanta ba sa buƙatar dukiyar Najeriya don azurta kansu.

Ta yi alƙawarin cewa za su yi aiki domin inganta ƙasar nan don amfanin kowa da kowa.

Daily trust

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Likitocin Jinya da Ungozoma sun janye yajin aiki – Ministan lafiya

Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Ƙasa (NANNM) ta...

Sarkin Hausawan Arewa, Amb. Balarabe Tatari, Ya Aike da Sakon Ta’aziyyar Buhari da Dantata

Sarkin Hausawan Arewa kuma Ambasadan Zaman Lafiya, Alhaji Balarabe...

INEC ta sanya ranar fara rijistar masu zabe a Nigeria

Hukumar zaɓen Najeriya ta ce nan gaba cikin wannan...