Yanzu-yanzu: An rage kudin shiga zaɓen kananan hukumomi na Kano

Date:

Daga Mukhtar Yahya Shehu

 

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano ta rage kudin takardar tsayawa takara.

Shugaban hukumar zaben ta jiha faefesa Sani Lawal Malunfashi ya sanar da haka yayin Taron masu ruwa da tsaki dangane da zaben kananan hukumomin jihar da ke tafe a wata mai kanawa.

Zaɓen Kano: NDLEA ta fitar da sakamakon yan takara 20 da aka yiwa gwajin shan kwaya

Ya ce rage kudin takardar tsayawa takara ya biyo bayan umarnin kotu bayan da wasu jam’iyyun adawa sun shigar da hukumar Kara dangane da yawan kudin na takardar tsayawa takara.

Farfesa Sani Lawal Malunfashi ya ce a halin yanzu hukumar zaben ta jiha ta mayar da kudin takardar tsayawa takara a matakin Shugaban hukumar hukuma da mataimakinsa naira miliyan 9 sakamakon naira miliyan 10 a baya, yayin da Kuma takardar tsayawa takara a matakin kansila naira miliyan 4 sakamakon naira miliyan 5 a baya.

Ya ce a halin yanzu hukumar ta kammala shirye shiryen fara sayar da wadannan takardu daga ranar Litinin Mai zuwa wato 15; ga wannan wata.

Farfesa Sani Lawal Malunfashi ya yaba wa jam’iyyun siyasa bisa yadda suke bai wa hukumar hadin Kai musamman babbar jam’iyyar adawa a nan Kano ta APC bisa amincewa da shiga zaben na kananan hukumomin jihar a ranar Asabar 26 ga watan oktoba mai zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...

Yadda Buhari ya ƙi karɓar kyautar jirgi lokacin yana kan mulki – Garba Shehu

  Mai magana da yawun tsohon Shugaban Najeriya Muhammad Buhari,...

Gwamnan Kano ya kafa kwamitin bincike kan kwamishinan da ya tsayawa wanda ake zargi da harkar kwayoyi

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...