Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Kano ta Sanya Ranar Komawa Makarantun Firamare da Sakandire

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Gwamnatin jihar Kano ta amince da ranar Lahadi, 15 ga Satumba, 2024, a matsayin sabuwar ranar da ɗaliban makarantun firamari da sakandire za su koma karatu domin fara zangon farko na shekarar 2024/2025 ga dukkan makarantun kwana a jihar.

Dalibain sauran makarantu na jeka ka dawo kuwa za su koma ranar Litinin 16 ga Satumba, 2024.

Idan dai ba a manta ba kadaura24 ta rawaito, kwamishinan ilimi na jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa ya sanar da dage komawa makarantun a ranar Asabar 7 ga watan Satumba.

Jerin sunayen yan takara 38 da NNPP ta tsayar a zaɓen shugabannin kananan hukumomin Kano

A wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar, Balarabe Abdullahi Kiru ya sanya wa hannu, kwamishinan ya bukaci iyaye da su tabbatar da cewa ya’yansu sun koma makarantunsu a ranar da aka ambata domin a ranar za su ci gaba da aiki domin tabbatar da cikakken bin doka.

Haka kuma ya shawarci dalibai da su guji shiga makarantunsu da duk wani abu da ya sabawa doka, kamar wukake ko reza, da dai sauransu.

Sanarwar ta sake jaddada kudurin gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusif na ganin kowane yaro ya samu ilimi mai inganci.

Inganta Aiki: NUJ za ta yi aikin haɗin gwiwa da Rundunar yan Sanda a Kano

“Gwamnati na daukar matakai masu kyau wajen samar da ingantaccen yanayi na koyo da zai zaburar da karfafawa daliban mu kwarin gwiwa a fannin ilimi,” in ji sanarwar.

Sai dai sanarwar ta bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da bai wa ma’aikatar hadin gwiwa, tare da ba su tabbacin cewa gwamnati na daukar dukkanin matakan da suka dace domin tabbatar da ingantaccen yanayin koyo da koyarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...