Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shekaru goma sha biyu da kafa Jami’ar Maryam Abacha American University of Niger (MAAUN) da ke Maradi a Jamhuriyar Nijar, ta samar da shugabannin kwalejojin aikin jinya guda biyar a jihohin Borno da Yobe da Bauchi.
Dr. Hadiza Sabo wadda ta kammala karatun jinya a jami’a ita ce shugabar kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma ta Shehu Sule a Damaturu, jihar Yobe.
Hakazalika, Dakta Hadiza Yahya tana aiki a matsayin shugabar, College of Nursing Sciences a Maiduguri, jihar Borno, yayin da Dr. Rakiya Saleh ita ce Shugabar kwalejin koyar da aikin jinya da ke Bauchi, jihar Bauchi. Dukkanin waɗanda aka ambata din duk sun yi digirinsu na farko da na biyu a MAAUN.
Tsagin Sadiq Wali Sun yi fatali da zaɓen shugabannin PDP na Mazabun Kano
Bugu da kari, Kiloh Nifor wanda shi ne Shugaban, College of Nursing Sciences da ke Jalingo, jihar Taraba, da Dokta Yusuf Bello, Shugaban, Kwalejin Kimiyyar jinya ta Jihar Kaduna, suma tsofaffin daliban jami’ar ne.
MAAUN, wadda aka kafa a shekarar 2013, mallakin Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ce, wani mai taimakawa al’umma kuma masanin harshen Faransanci.
Jaridar Politics Digest ta kuma ruwaito cewa, tsangayar harkokin Shari’a ta Premier Ivory Tower, wacce aka kafa a shekarar 2015 kawai, ta samar da sama da mutane 400 da suka kammala karatun shari’a, inda sama da dari daga cikinsu tuni suka halarci makarantar koyon aikin Lauyoyi ta Najeriya.
Bugu da kari, Sama da masana kimiyyar dakin gwaje-gwaje 1,000 da jami’ar MAAUN ya samar suna aiki a Najeriya a halin yanzu, yayin da kasa da 700 daga cikinsu ke aiki a kasashen waje.
Idan dai za a iya tunawa, Jami’ar ita ce ta farko da ta fara ba da digiri a fannin aikin jinya a jamhuriyar Nijar, inda dubban jami’an jinya suka yi tururuwa don neman ilimin jami’a a fannin daga kasashe daban-daban.
“Fara gudanar da Digiri a fanni aikin jinya a Jami’ar ya kara yawan wadanda suka kammala karatun jinya a Najeriya sosai, jami’ar ta fara bayar da damar yin Digiri a aikin jinya a shekarar 2012 kuma zuwa yanzu ta yaye sama da dalibai 2,000 da suke gudanar da ayyukansu a asibitoci daban-daban a Najeriya da kasashen waje,” in ji shugaban jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo.
Dalilin da yasa mai magana da yawun Shugaban ƙasa Tinubu ya Ajiye aikinsa
Barista Umar Isa Sulaiman, malami a tsangayar harkokin shari’a a MAAUN, a lokacin da zantawa da jaridar Politics Digest ya ce tsangayar ta fara aiki a shekarar 2013, ya ce: “Dalibanmu da suka kammala karatu yanzu da yawansu su na aiki a hukumomin gwamnati da ma’aikata daban-daban, wasu kuma alkalai ne na kotun shari’a, wasu kuma alkalai ne a kotunan majistiri, wasu kuma suna aiki har a kotun kolin Najeriya.
“Har ila yau, da yawa daga cikin dalibanmu kuma suna aiki a matsayin lauyoyi masu zaman kansu, muna haduwa da su a gaban kotuna daban-daban. Zan iya gaya muku cewa suna aiki sosai a matsayin masu bayar da shawarwari.”
Bugu da kari, jami’ar mallakin Farfesa Adamu Gwarzo ta yi tasiri sosai a rayuwar ‘yan Najeriya da dama.
Wani tsohon dalibin MAAUN da ya kammala karatun aikin jinya Hamisu Iliyasu, wanda ya fito daga Jihar Sakkwato, ya shaida wa wannan jarida cewa akwai da yawa daga cikin abokan karatunsu da zama daraktoci wasu kuma sun zama Shuwagabannin Ma’aikatan jinya da dama a Najeriya.
“Ka san jami’o’in Arewa ba sa yin dirigi a fannin aikin jinya, ko dai ka je Kudu ko kuma ka yi ritaya a matakin albashi na 14 idan kana ma’aikacin gwamnati, amma jami’armu ta Maryam Abacha American University ta kawon mana dauki sosai kuma muna gode mata,” inji shi.
A cewar Dokta Kabiru Mahmud, ma’aikacin Sashen Kimiyyar dakunan gwaje-gwaje a Jami’ar MAAUN, “Wannan babbar jami’ar tamu ta taimaka wajen kara yawan masana kimiyyar dakin gwaje-gwaje, ba a Arewacin Najeriya kadai ba, har ma a kasar baki daya, domin mun yaye dalibai da dama daga ko’ina cikin kasar nan.
“Wasu sun fito ne daga Legas, Benin, da Ibadan, a zahiri zan iya gaya muku cewa Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijar ce ta fi kowacce matasa kwararrun masana kimiyyar dakunan gwaje-gwaje a Najeriya.
“A da, da kyar mutum ya samu wanda ya yi digiri a wannan fanni, sai dai Difloma, amma MAAUN ta zo ta ba da dama ga dimbin daliban da suka kammala karatun digiri, ka je cibiyoyin kiwon lafiya na tarayya da ke fadin kasar nan, zai yi wuya ka rasa wanda ya kammala wannan jami’ar ta MAAUN.”
Binciken da wannan jarida ta yi ya nuna cewa a halin yanzu wasu tsofaffin daliban MAAUN na aiki a Asibitin kasa da ke Abuja da kuma Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke AKTH a Jihar Kano.
Jami’ar bisa ga binciken jami’ar tana da mafi yawan ma’aikatan jinya da ke aiki a Kanada, Amurka da sauran ƙasashen waje daga Afirka ta Yamma.