Tsagin Sadiq Wali Sun yi fatali da zaɓen shugabannin PDP na Mazabun Kano

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Tsagin Sadiq Wali dake cikin jam’iyyar PDP a jihar kano sun yi fatali da yadda aka gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar na mazabu a fadin jihar.

” Ba mu gamsu da yadda aka gudanar da zaben ba, saboda an gudanar da zaben ba tare da bin ka’idoji ba, Sannan kuma ba a gudanar da zaben a bayyane ba Sannan an ware wasu shafaffu da mai da aka fifita yayin zaɓen a jihar kano”.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban tsarin na Sadiq Wali wato Munhammina Bako Lamido wadda kuma aka aikowa kadaura24 a ranar asabar.

Dalilin da yasa mai magana da yawun Shugaban ƙasa Tinubu ya Ajiye aikinsa

Bangaren Sadiq Aminu Wali na jam’iyyar PDP reshen jihar Kano na fatan kin amincewa da taron mazabun da aka gudanar a jihar a yau. Mun yi imani da cewa tsarin ba shi da cikakkiyar fa’ida, haɗa kai, da adalci waɗanda ke da mahimmanci don tabbatar da manufofin dimokuradiyya na babbar jam’iyyarmu.

“Akwai matukar damuwa yadda da gangan aka cire manyan masu ruwa da tsaki da ’ya’yan jam’iyya na halal wajen gudanar da taro, da kuma wasu kura-kurai da aka samu a lokacin zaɓen. Wannan tsarin bai yi dai-dai da tsarin dimokuradiyya ba, kuma ya ci karo da ka’idojin da jam’iyyar PDP ta tsayar da kuma kudurinmu na ganin an bai wa kowanne dan jam’iyya dama daidai da kowa”. A cewar Sanarwar

Farashin man fetur: NNPC ta baiwa Matatar Ɗangote dama

Sanarwar ta ce Sadiq Aminu Wali, jagoran mu, ya nuna rashin jin dadinsa kan saba ka’idojin jam’iyyar. Duk da kokarin da ake yi na tattaunawa da bangarorin jam’iyyar da abin ya shafa don warware matsalolin da suka kunno kai a gaban majalissar, an yi watsi da abubuwan da suka dace da mu, wanda ya haifar da kura-kurai a yau.

“Muna kira ga shugabannin jam’iyyar PDP na kasa da su gaggauta tsoma baki tare da daukar matakan da suka dace don magance matsalolin da aka fuskanta a yau. Wannan zai taimaka wajen samun hadin kai da mutuncin jam’iyyar, musamman a daidai lokacin da ake tunkarar zabe mai muhimmanci a jihar Kano”.

Hon. Munhammina Bako Lamido

Sanarwar ta kara da cewa”Bangaren mu ya jajirce wajen tabbatar da tsarin dimokuradiyya, bin doka da adalci, muna kuma kira ga magoya bayanmu da su kwantar da hankalinsu yayin da muke neman gyara ta hanyoyin da suka dace”.

“Muna kara jaddada biyayyarmu ga jam’iyyar PDP da manufofinta kuma za mu ci gaba da kokarin ganin mun gina jam’iyya mai karfi da hadin kai a jihar Kano”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...