Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Mai magana da yawun shugaban kasa Bola Tinubu, Chief Ajuri Ngelale ya ajiye aiki sakamakon rashin lafiya.
Ajuri, ya bayyana hakan ne a wata takaitacciyar sanarwa da ya fitar a yau Asabar.
“A ranar Juma’a, na mika takarda ga shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa, inda na ke shaida masa cewa na tafi hutu na sai-baba-ta-gani domin mayar da hankali kan batun rashin lafiya wanda hakan abun damuwa ne ga ahali na.
Yadda za ku sayi Shinkafar Tinubu akan Naira dubu 40 kowanne buhu
” A yayin da na ke godiya kan wannan nauyi da aka dora min wanda yanzu ya kai matakin yanke shawarar dakatawa da aikina a matsayin mai baiwa shugaban kasa shawara a fannin yada labarai kuma mai magana da yawunsa; jakada na musaaman ga shugaban kasa a fannin sauyin yanayi kuma shugaban kwamitin shugaban kasa kan shirin Evergreen.
YANZU-YANZU: Tinubu ya magantu kan karin farashin man fetur Nigeria
“Na dau wannan matakin ne bayan tuntubar iyalina a yayin da rashin lafiya ya tsananta a gida na.
Zan dawo bakin aiki da zarar waraka ta samu kuma lokaci ya bada dama,” in ji Ngelale.