Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Kungiyar Samarin Tijjaniyya ta Kasa tayi Allah wadai tare da nuna rahin Jin dadinta bisa tashin gwauron zabi da man fetur yayi a fadin Kasar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kungiyar ta fitar sakamakon sanarwar data fito na Kara farashin mai da kamfanin Samar da man fetur na Kasa yayi.
Sanarwar da Sakataren Kungiyar Samarin Tijjaniyya ta Kasa Shehu Tasiu Ishaq da sakataren yada labarai na Kungiyar Abubakar Balarabe Kofar Naisa suka sanyawa hannu tace bisa la’akari da halin da “Yan kasa ke ciki akwai bukatar a duba lamarin.
Karin kudin mai: Kayan masarufi kan iya tashi – kungiyar masu masana’antu
Kungiyar ta bukaci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya rage farashin Man fetur din a maimakon Kara farashin sa, domin saukakawa al’umar Najeriya.
Sanarwar daga nan sai ta bukaci al’umar Najeriya su cigaba dayin addu’oi na neman samun sassaucin al’amura da samun cikakken tsaro da wadatar arziki a Kasa baki daya.