An Karrama Mai Magana Da Yawun Gwamnan Kano Kan Batun Taimakawa Daliban Dawaki Tofa

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

Kungiyar Dawakin Tofa Academic Forum (DAF) da gidauniyar ilimi ta Dawakin Tofa (DETFnd) sun karrama Sunusi Bature Dawakin Tofa bisa namijin kokarin da yake yi na ciyar da dalibai gaba a karamar hukumar Dawakin Tofa.

Sunusi Bature wanda shi ne mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya samu wannan karramawa ne a wata ziyarar da kungiyar ta kai ofishin sa a ranar Talata.

Kungiyoyin sun yi yabon ne ta wata wasikar godiya da Dr. Mamunu Mustapha ya gabatar a madadin kungiyoyin biyu.

Wasikar ta bayyana yadda Sanusi Bature ya ke bayar da tallafi ga daliban Dawakin Tofa, musamman wadanda suka yi karatun digiri a Jami’ar Bayero Kano (BUK).

Talla
Talla

Gudunmawar da ya bayar, wanda ya hada da biyan kudaden rajista na Shekarar 2023/2024, ya fitar da dalibai da yawa daga matsalolin kudi, ya ba su damar mayar da hankali kan karatun su.

Baya ga tallafin da yake baiwa daliban BUK, Sunusi Bature ya fadada har zuwa sauran manyan makarantu.

Sabuwar Badakala a Kano: An kama Kantomomi 3 da wasu 19, An kuma Saki Dan Kwankwaso

Ya bayar da irin wannan taimako ga daliban da ke karatu a Makarantar Kimiyyar Kiwon Lafiya a Jihar Kano da ke Gwamai, tare da sauran al’amuran da suka shafi cigaban ilimi ga matasa a karamar hukumar.

DAF da DETFnd sun jaddada cewa Sunusi Bature ya jajirce wajen inganta harkokin ilimi a garin Dawakin Tofa ya taimaka matuka wajen ganin an samu karin daliban da suke karatun boko a yankin.

Sun bukace shi da ya ci gaba da kokarinsa na daukaka matsayin ilimi da samar da damammaki ga matasa a cikin al’umma .

Wannan karramawa ta nuna irin gagarumar rawar da shugabanni irin su Sunusi Bature ke takawa wajen ci gaban al’umma .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Obasanjo, Atiku, Obi da sauransu sun halarci taron kaddamar da littafin Sule Lamido

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, da...

Gwamna Kano zai Baiwa Malaman Makarantu Bashin Ababen Hawa Motoci Naira Miliyan 200 A Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf...

Za mu yi aikin hanyar Utai zuwa Kademi – Shugaban karamar hukumar Wudil

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Wudil Abba Muhammad...

Malaman addinin musulunci a Kano sun bayyana matsayarsu kan hana hirar siyasa kai tsaye a gidajen radio

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Majalisar limaman masallatan juma'a ta jihar...