Sabuwar Badakala a Kano: An kama Kantomomi 3 da wasu 19, An kuma Saki Dan Kwankwaso

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar kano ta kama wasu shugabannin riko na kananan hukumomi uku bisa zargin badakalar kwangilar ruwa ta Naira miliyan 660.

Wata majiya a hukumar ta bayyanawa Daily Trust cewa, Kantomomin kananan hukumomin uku da ake bincika sun bayyana cewa sun karkatar da wasu makudan kudade zuwa asusunsu na kashin kai.

Kantomomin da aka garkame sun hadar da kantomar karamar hukumar Kiru Abdulaziz Sulaiman da Basiru Abubakar na karamar hukumar Bebeji da kuma Gambo Isa shugaban riko na karamar hukumar Garko.

Talla
Talla

Har ila yau, mutane 19 a halin yanzu suna tsare kuma ana yi musu tambayoyi. Sun hada da ma’aji, HOD na WASH da sauran manyan jami’an kananan hukumomi daban-daban.

Daga cikinsu akwai Nura Uba Sani, Muhammad Sani, Usman, Ibrahim Sani, Usman Yusha’u, Muhammad A Shehu, Ismail Yusuf, Muhammad Jamilu, Sani, Kabiru Akilu Kawo, Nasir Adamu, Basiru, Abubakar, Danlami Mu’azu Sa’idu. , Abdullahi, Muhammad Yako, Abubakar Muhammad, Abba Abdullahi, Gali Abdulkadir Jauro, Bashir Ibrahim Fanda, Garzali Abdu Sulaiman da Ibrahim Danguda.

Ana zargin su da sanya kudaden gwamnati a asusunsu na kashin kai a wasu lokutan ma da cirer tsabar kudin .

Majiyar kadaura24 ta fahimci cewa an kwato wasu miliyoyi kudade daga hannunsu yayin da ake ci gaba da bincike tare da kokarin kwato wasu.

Gyaran bangaren Lafiya: Gwamna Yusuf zai samar da hukumar kula da masu magungunan gargajiya a Kano

Sai dai kuma an bayar da belin Kantomomin ukun, amma har zuwa karfe 10 na daren jiya alhamis ba su cika sharuddan belin ba.

Badakalar magunguna: Dan Kwankwaso zai Maka ICPC, EFCC da PCACC a gaban Kotu

Rahotanni sun nuna cewa Naira miliyan 660 na daga cikin Naira biliyan 1.1 da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince wa kananan hukumomi 44 don magance matsalolin da suka shafi ruwa da magunguna.

Yarjejeniyar ta shafi ayyukan da aka tsara a watan Agusta, Satumba da Oktoba 2024, tare da ware Naira biliyan 1.1 a kowane wata, wanda ke ba da Naira miliyan 25 ga kowace karamar hukuma.

Daga cikin Naira miliyan 25 da aka amince da mika wa kowace karamar hukuma a watan Agusta, an gano cewa an umurci shugabannin rikon da su tura Naira miliyan 10 kowannensu zuwa asusun Novomed Pharmaceuticals, wani kamfani mallakin Musa Garba, dan kanin ​​Sanata Rabiu Kwankwaso jagoran tafiyar Kwankwasiyya.

Hukumar yaki da cin hancin ta gana da shi a ranar Alhamis, ya amsa gayyatar hukumar, Amma an tsare shi amma an bayar da belinsa da misalin karfe 9 na dare a ranar Alhamis.

Majiyoyi sun ce an umarce shi da ya koma ofishin hukumar a ranar Litinin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An dakatar da Shugaba da Sakataren kungiyar APC X Eagle forum

Kwamitin zartarwa na kungiyar APC X Eagle forum ya...

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...