Gyaran bangaren Lafiya: Gwamna Yusuf zai samar da hukumar kula da masu magungunan gargajiya a Kano

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya samu lambar yabo daga kungiyar kwararrun likitocin magungunan gargajiya ta Najeriya bisa kokarin da yake yi na hada kai da wayar da kan mambobinta sama da 5,000 don tallafawa ayyukan kiwon lafiya na jihar.

Gwamnatin jihar ta zabo tare da tantance masu sana’ar sayar da magungunan gargajiya sama da 5,000 da aka ba su takardar shaidar yin maganin gargajiya a Kano daga kananan hukumomi 28 na jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24 ranar Alhamis.

Badakalar magunguna: Dan Kwankwaso zai Maka ICPC, EFCC da PCACC a gaban Kotu

Shugaban kungiyar na kasa Alhaji Maikudi ya bayyana irin kyakkyawar alakar da ke tsakanin kungiyar da jihar, inda ya danganta hakan da kokarin Gwamna Yusuf .

Shugaban kungiyar na kasa ya bayyana jin dadinsa a lokacin kaddamar da kwamitin yaki da cututtuka masu yaduwa na jihar Kano, wanda aka gudanar a fadar gwamnatin jihar Kano.

Ya kuma yabawa Gwamnan kan yadda ya farfado da fannin kiwon lafiya da kuma ba da kulawa ta musamman ga masu Sana’ar magungunan gargajiya.

Tinubu ya yi wa Nigeria illar da za a dade ba a gyarata ba – Atiku Abubakar

Ya kuma nuna jin dadinsa da irin tallafin da gwamnati ta ba su, wanda hakan ya baiwa masu aikin likitanci damar gudanar da aiki yadda ya kamata.

Alhaji Maikudi ya kuma bukaci Gwamnan jihar da ya kafa hukumar kula da magungunan gargajiya domin kara shigar da magungunan gargajiya cikin tsarin kiwon lafiya na jihar.

A nasa jawabin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yaba da gudunmawar da masu magungunan gargajiya ke bayarwa a fannin kiwon lafiya na jihar.

Ya kuma jaddada kudirin gwamnatinsa na inganta harkokin kiwon lafiya tare da jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin ayyukan masu maganin gargajiya da likitocin zamani.

Gwamnan ya bayyana shirye-shiryen tallafawa masu sayar da magungunan gargajiya ta hanyar basu horo na musamman da samar da hadin gwiwa tsakanin su da cibiyoyin kiwon lafiya, da kuma kafa hukumar da zata rika lura da aiyukansu.

Ya yin hakan zai kara inganta aiyukansu ta yadda zasu cigaba da ba da gudunmawa wajen kula da lafiyar al’umma da kuma haɗa su da tsarin kula da lafiya na jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...