Badakalar magunguna: Dan Kwankwaso zai Maka ICPC, EFCC da PCACC a gaban Kotu

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Dan kanin jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, Musa Garba Kwankwaso, ya ce zai garzaya kotu domin kalubalantar matakin da wasu hukumomin yaki da cin hanci da rashawa uku suke dauka akansa.

Kwankwaso ya bayyana haka ne jim kadan bayan ya amsa gayyatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar (PCACC) ta yi masa a ranar Alhamis tare da lauyoyinsa.

Daily Trust ta ruwaito cewa Hukumar PCACC ta shirya wata ganawa da Manajan Daraktan Kamfanin Magunguna na Novomed, Musa Garba Kwankwaso, kan badakalar kwangilar samar da magunguna ta miliyoyin Naira.

Tinubu ya yi wa Nigeria illar da za a dade ba a gyarata ba – Atiku Abubakar

Wasikar mai dauke da sa hannun shugaban sashin ayyuka na hukumar CSP Salisu Saleh a madadin shugaban hukumar ta bayyana cewa, “Hukumar tana binciken laifin karya sashe na 31 da 33 na dokar sayo kayan gwamnati da kuma tsarin kula da harkokin kudi dangane da kwangilar da ma’aikatar ta bayar ga Kananan Hukumomin Jihar Kano ga Kamfanin ku (Novomed Pharmaceuticals) domin samar da magunguna ga Kananan Hukumomi 44.”

Ana gudanar da binciken ne a kan kwangilar magunguna ta Naira miliyan 440.

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta sami umarnin hana cire kudi a asusun Novomed Pharmaceuticals, inda ta toshe sama da Naira miliyan 160 yayin da take kokarin kwato sauran kudaden.

Alkalin alkalan Nigeria , Ariwoola ya yi ritaya

Da yake magana, lauyan Kwankwaso, Barista Okechukwu Nwaeze, ya ce, “Hukumomi uku da suka hadar da ICPC, EFCC da PCACC suna bincike akan mutum daya kan laifi iri daya, Kuma dukkaninsu sun mika masa goron gayyata bana jin kundin tsarin mulkinmu ya yarda da hakan.

“Mun kai wannan magana gaban kotu, domin ta warware matsalar domin batun akwai rudarwa a cikin sa.

“Mun yanke shawarar tafiya kotu domin warware dambarwar ta yadda hukumomi uku ba za su iya bincike akan mutum daya kuma akan laifin daya.”

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Dan Bello ne dai ya fara fallasa cewa kananan hukumomin Kano suna baiwa kamfanin Novomed kwangilar Naira miliyan 10 wannensu domin sayo Magunguna, a cikin wani bidiyo da ya saki, sai dai gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce bai sance da cewa ana ba da kwangilar ba, Sannan kuma ya baiwa hukumar yaki da cin hanci da rashawar ta jihar ta gudanar da bincike tare da mika masa rahoton binciken domin daukar matakin da ya dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...