Bayan Cire Shugaban NAHCON, Tinubu ya nada wani malamin Addini daga Kano

Date:

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Farfesa Abdullahi Saleh Usman a matsayin shugaban hukumar kula da alhazai ta Nigeria (NAHCON).

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Bola Tinubu Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.

Da dumi-dumi: Tinubu ya bayar da umarnin biyan tallafin man fetur – Rahoto

Farfesa Abdullahi Sale fitaccen malamin Addinin musulunci ne wanda ya yi digirinsa na farko a cibiyoyin ilimi na Musulunci guda biyu – Jami’ar Madina da Jami’ar Peshawar da ke Pakistan.

Ya kuma kware wajen gudanar da aikin Hajji, inda ya taba rike mukamin Shugaban Hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar Kano, kuma ya samu nasarar mai tarin yawa a lokacinsa.

Rushewar gini ya kashe wasu yara biyu ƴan gida ɗaya a Kano

Sabon mukamin nasa zai fara aiki ne bayan Majalisar kasa ta amince da nadin.

Shugaban ƙasar ya yiwa sabon shugaban hukumar ta NAHCON fatan alkhairi tare da fatan zai gudanar da aikinsa bisa gaskiya da rikon amana ga alhazan Nigeria .

Idan dai za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito ana zargin tsohon shugaban hukumar ta NAHCON Jalal Arabi da almundahanar kudade bayan kammala ibadar aikin hajjin bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...