An zargi Hadimin Gwamnan Kano da yada labarin karya kan ganawar Sanata Barau da tsaffin shugabannin LG

Date:

Daga Kamal Yahaya Zakaria

 

Kungiyar Maliya Media Reporters ta zargi mai Magana da yawun gwamnan jihar kano Sanusi Bature Dawakin Tofa da ya yada labarin karya game da ziyarar da tsofaffin shugabannin kananan hukumomin Kano na jam’iyyar APC suka kaiwa Sanata Barau Jibril.

Kungiyar ta ce Labarin mai take ” Tsofaffin Ciyamomin jam’iyyar APC na jihar kano sun yiwa Ganduje bara’a tare da yin mubaya’a ga Sanata Barau Jibril” kungiyar ta ce labarin karya ne ba shi da tushe ballantana makama.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Maliya Media Reporters Com. Adamu Abdullahi karkasara ya aikowa kadaura24.

Sabon Rikici Ya Kunno Kai A Jam’iyyar APCn Kano

Wannan hoton ya nuna cewa Tofa ne ya bada labarin a wani group din Whatsapp mai suna Kano News Room da misalin karfe 4:32 na yammacin ranar Juma’a, inda ya bukaci ‘yan jarida da su danganta labarin ga wasu majiyoyi da ba a san sunansu ba.

“Muna yaba wa ’yan jarida bisa yadda suke nuna ƙwarewa wajen bin ka’idojin aikin jarida. Muna kuma kira ga editoci da mawallafa na kafafen yada labarai na yanar gizo da sauran su da su rika lura da labaran karya” inji karkasara

Karin haske, a ranar Alhamis din da ta gabata ne tsoffin shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Muhammad Baffa Takai, tsohon shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomin Najeriya (ALGON) reshen jihar Kano suka halarci wani taron a Abuja domin karrama mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau I Jibrin bisa kafa hukumar raya yankin arewa maso yamma (NWDC).

Musamman ’yan siyasa da talakawa suna yaba wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan amincewa da kudurin dokar NWDC da Sanata Barau ya dauki nauyi. A duk tsawon taron, ba a tattauna kan APC ko wata jam’iyyar siyasa a Kano ko a matakin kasa ba; a maimakon haka taron ya mayar da hankali ne kan yadda za a jawo karin ayyuka a jihar kano.

Babban Hadimin Gwamnan Kano ya ajiye Mukaminsa tare da Komawa APC

“Amma abun takaici mai magana da yawun gwamnan kano shi da baya wajen taron amma yayi karya, don haka muna kira ga Tofa da ya daina yada labaran karya wadanda za su haifar da rashin hadin kai a tsakanin shugabanninmu na Kano. Kamata ya yi a kara wa shugabanninmu kwarin guiwa ba tare da la’akari da jam’iyyun siyasa ba, su hada kai don ci gaban Kano da kasa baki daya bisa tsarin sabunta fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Muna fata Gwamna Abba Kabir Yusuf zai gaggauta umartar Sanusi da ya daina yada labaran karya domin maslahar Jihar mu. Dole ne kowa ya tashi tsaye domin tunkarar kalubalen da ke gabanmu a Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar cigaban Ilimi da gyaran tarbiya ta unguwar zango ta shirya taron kan tarbiyya da tsaro

Daga Rahama Umar Kwaru   Wani Malami a jami'ar Bayero dake...

Gwamnatin Kano ta sanar da Ranar Fara hutun zangon Karatu na 3 ga ɗaliban jihar

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da...

Gwamnatin Kano za ta fara jiyo ra’ayoyin al’umma kafin gudanar da duk wani aiki a jihar – Bilkisu Indabo

Daga Samira Hassan   Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin nan...

Kwankwaso ya gana da Tinubu a fadar shugaban kasa

Daga Nasiba Rabi'u Yusuf   Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso,...