Daga Umar Ibrahim Kyarana
Mai Martaba Sarkin Karaye Alhaji Muhammad Maharaz ya Amince da na din, wasu daga cikin yan majalisar masautar domin cigaba masarautar Karayen.
Wannan shi ne karon farko da sarkin ya yi nade-nade tun bayan da gwamnan jihar kano ya amince da nadin sarkin a matsayin sarki mai daraja ta biyu.
Sabon Rikici Ya Kunno Kai A Jam’iyyar APCn Kano
Sarkin ya amince da nadin Alh. Balarabe Surajo Karaye a matsayin Wamban Karaye kuma Babban Dan Majalisar Sarki Senior Councillor a Masarautar Karaye, sai Alh Ibrahim Muhammad Karaye a Matsayin Chiroman kuma Shugaban Ma’aikatan Masarautar Karaye, sai Malam Muktar Ishak Idiris a Matsayin Sakataren Masarautar Karaye.
Babban Hadimin Gwamnan Kano ya ajiye Mukaminsa tare da Komawa APC
Jama’ar Masarautar Karaye sun yi murna da wannan Matsayi da Allah ya Baiwa wadannan mutane masu kwazo da kokarin kawo cigaba a yankin Masarautarsa Karaye .
Al’ummar masarautar sun kuma yabawa mai martaba Sarkin Karaye Alh. Muhammad Maharaz bisa kokarin sa na Rungumar kowa domin samar da cigaba a yankin.