Yadda aka bankado haramtattun matatun man fetur 63 a Nigeria

Date:

Babban kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL, ya ce ya bankaɗo wuraren 63 da ake tace mai fetur ba bisa ƙa’ida ba a cikin makon da ya gabata.

Cikin wani rahoton kamfanin da aka yaɗa a gidan Talbijin na Nigeria NTA, ya nuna cewa an gano haramtattun bututan mai 19 da kuma wurare 63 da ake tace mai ba bisa ƙa’ida ba.

An Sace muhimman takardun tuhume-tuhumen da ake yi wa Ganduje – Gwamnatin Kano

Rahoton kamfanin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan jinkirin fara aikin matatar mai ta birnin Fatakwal, ba kamar yadda aka tsara tun farko ba.

Matatar ta Fatakwal – da ke ƙarƙashin kamfanin NNPCL – ta kasa fara aiki bayan an ɗage lokacin fara aikin nasa har sau shida.

Ma’aikatar albarkatun man fetur ta Najeriya da kamfanin mai na NNPCL sun alƙawarta fara aikin matatar cikin wannan wata, to sai dai alamu na nuna cewa ba lallai ne matatar ta fara tace man cikin wannan wata ba.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...