Daga Halima Musa Sabaru
Sabanin ikirari da gwamnatin jihar Kano ta yi na cewa jam’iyyar APC ce ta dauki nauyin gudanar da zanga-zangar da aka yi a jihar Kano kwanan nan, maimakon haka, shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ce ta dauki nauyin gudanar da zanga-zangar don bata sunan gwamnatin shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labarai na shugaban jam’iyyar APC na kasa, Mista Edwin Olofu, a ranar Alhamis a Abuja, ta bayyana cewa wasu sahihan rahotannin sirri sun nuna cewa zanga-zangar da ta rikide zuwa fashe-fashe da sace-sace, gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ce ta dauki nauyi kai tsaye.
“Abin takaici ne yadda gwamna mai ci zai tada irin wannan rikici da tashin hankali a jiharsa, tare da jefa rayuka da dukiyoyin al’ummar da ba su ji ba ba su gani ba cikin hadari.
A karon farko Farashin Kayan Abinchi ya sauka a Nigeriya
“Mun yi Allah wadai da wannan hali na rashin da’a, wanda wani yunkuri ne na kawo cikas ga zaman lafiya a Kano, da gurgunta zaman lafiya da tsaro a yankin, musamman don batawa Shugaban kasarmu suna.
“Muna bukatar gwamnatin tarayya ta hannun jami’an tsaro da abin ya shafa, ta gaggauta gudanar da bincike mai zurfi kan yadda gwamnatin jihar Kano ke da hannu a cikin wannan mummunan lamari.
“Wajibi ne a gurfanar da masu daukar nauyin wannan tashin hankalin a gaban kuliya domin tabbatar da cewa hakan bai sake faruwa ga sauran jihohin ba.”
Bugu da kari kuma, mun gano zargin da ake yi cewa masu zanga-zangar sun kwashe tare da arcewa da wasu ‘takardu masu inganci da suka shafi zargin cin hanci da ake yi wa tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin mara tushe balle makama.
“Me ya faru da takardun tare da lauyoyin gwamnati, gwamnatin jihar ba ta da tunanin yadda za ta tafiyar da al’amuran jihar, kuma a koda yaushe ta koma yin fatali da zarge-zargen cin hanci da rashawa da dama a kan tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da gwamnatinsa. iyalan da suka yi wa jihar hidima.
“Wannan ikirari ba wani abu ba ne illa kokarin da gwamnatin Gwamna Yusuf ke yi na kawar da hankulan su daga rikicin da ya barke a jihar.
“Maganar cewa za a iya kwashe irin wadannan muhimman takardu yayin zanga-zangar ba wai kawai an yi shi ba ne, har ma yana nuni da yadda jihar ke kara gazawa wajen tafiyar da harkokin tsaro da na shari’a.
An ƙayyade kuɗin fom din tsayawa takara a zaɓen ƙananan hukumomin Kano
“kowa ya sani gwamnan kano shi ne ya kirawo masu zanga-zangar, ya ce zai karbe su, amma abin takaici shi ne yadda wadanda gwamnan ya gayyato suka fara fasa kayan gwamnatin tarayya”.
Bayan ya jagorance su, yanzu ya tabbata ga kowa da kowa cewa gwamnatinsa ce ta dauki nauyin wannan zanga-zanga da ta faru a Kano.
Ya kamata Gwamna Yusuf ya fahimci cewa magana da ayyukan shugabanni suna da nauyi kuma suna haifar da mummunan sakamako idan ba a yi su a inda ya dace ba.
“Muna tare da al’ummar Kano kuma muna kira ga dukkanin masu kishin jihar da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka da oda yayin da hukumomi ke gudanar da bincike.
“Jam’iyyar APC ta tsaya tsayin daka wajen samar da zaman lafiya, adalci, da kuma shugabanci na gari a fadin kasar nan.