Yadda aka sace Naira biliyan 50 daga asusun Gwamnatin Kano

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

 

 

Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta bankaɗo badaƙalar satar kuɗi sama da Naira biliyan 50 a ƙananan hukumomi 44 da ake jihar.

Shuagaban hukumar, Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce hukumar ta kuma gano wata badaƙalar Naira miliyan 450 da aka sace daga asusun jihar da sunan sayen gidajen sauro masu ɗauke da magani.

Ya shaida wa mahalarta wani taron ƙara wa juna sani cewar, “Mun gano Naira biliyan 50 da aka sace daga asusun jiha, kuma ,ina da shaidu kimanin 145.

“Sannann mun gano waso gidaje da otel-otel masu alaƙa da kuɗaɗen satan da a biranen Dubai, London, da kuma Abuja.”

Mun kafa kwamiti don gano Inda aka boye Shinkafar da Tinubu ya turo Kano – Munnir Muhd

A cewarsa, da hukumar ta yi yunƙurin binciken wanda ake zargi da badakalar Naira miliyan 450 na gidajen sauro, amma ya garzaya kotu neman umarnin hana ta bincikar shi.

Muhyi ya bayyana wa mahalarta taron, waɗanda jami’an hukumomin yaƙi da rashawa ne daga jihar da ma tarayya cewa, kashi 80% na satar kuɗin gwamanti da ak yi a Jiahr Kano, an yi ne da sunan sayen kayan gwamnati.

Ya ce hanyoyin sun haɗa da aringizon farashi, sayen kasa da abin da aka tsara, ko ma rashin yin sayayyar bayan an biya kuɗaɗen.

Da yake jawabi, wakilin daraktan Hukumar EFCC Shiyyar Kano a taron, CSP Aminu Bashir, ya bayyana cewa kashi 95% na satar kuɗaɗen gwamnati ana yin su ne a wurin yin sayayya.

A Karon Farko Malam Shekarau ya Magantu kan Rikicin Masarautar Kano

Don haka ya shawarci jami’an gwamnati da su rika bin ka’idodi da dokokin yin sayayyar gwamnati domin guje wa fushin shari’a ko shiga rikici.

A nasa ɓangaren, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda mataimakinsa, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya wakilta, ya bayyana cewa, satar kuɗaɗen gwamnati ba ta yiwuwa sai da haɗin bakin jami’an gwamnati.

Ya ce gwamnatin Abba ba za ta lamunci satar kuɗin gwamanti ko rashawa ba, domin a cewarsa, Jihar Kano ta ga mummunar illar satar kuɗin gwamanti a shekaru takwas da suka gabata, wanda a hakan ya hana wa jihar samun cigaba.

Daily trust

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...

Mun gano yadda yan Bauchi ke mamaye dazukan Kano – Gwamnatin Kano

Daga Nazifi Dukawa     Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gano...