Zanga-zanga: Rundunar Sojin Nigeria ta kama Sojan da ya harbe wani yaro

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kama wani soja da ya kashe wani yaro dan shekara 16 mai suna Ismail Mohammed ta hanyar harbi a yayin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a jihar Kaduna.

An kashe yaron ne a ranar Talata lokacin da sojojin Najeriya suka shiga cikin garin Samaru da ke Zariya domin tarwatsa masu zanga-zangar. Jami’an tsaro na aiwatar da dokar hana fita da gwamnatin jihar Kaduna ta sanya.

Farashin kayan abinci na daf da karyewa a kasuwa — Kwastam

Rundunar sojin Najeriya a cikin wata sanarwa da kakakinta Onyema Nwachukwu ya fitar a daren ranar Talata, ta tabbatar da cewa an kama jami’in da ke da alhakin kashe yaron.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A ranar 6 ga watan Agustan 2024, sojojin Najeriya sun samu kiran gaggawa game da wasu matasa da suka taru a Samaru, suna kona tayoyi a kan hanya, tare da jifan jami’an tsaro.

Talla
Talla

“Dakarun sun isa wurin domin tarwatsa matasan don tabbatar da dokar hana fita. Da isar su wurin matasan sun yi yunkurin kai wa sojojin hari, lamarin da ya sa wani soja ya yi harbin gargadi. Abin takaici, hakan ya yi sanadiyar mutuwar Ismail Mohammed mai shekaru 16.

“An kama sojan a halin yanzu ana yi masa tambayoyi.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...