Da farko dai, a gaskiya babu hikmah da fiqhud daawa wajen fitowa karara (da sunan kishin Sunnah) a soki kokarin da wasu suke yi domin gangamin addua na Kasa “National Prayers” akan Allah ya kawo mana sauki a kan balain da ake ciki a kasar nan. Yanzu kuncin da ake ciki wane bai sanshi ba?
In dai abinda ma su “National Prayers” idan sun taru za su yi shi ne; Karatun Qurani, Zikr da adduo’i akan Allah ya yaye mana musiba da damuwar da muke ciki ne, to wannan ba bu laifi kuma ba bidiah bane! Kuma yana da asali ma a Shari’a musamman idan anyi Qiyasi akan al-Qunutu a lokacin nawazil (wani balai’) da kuma Sallar rokon ruwa.
Ko da yake Malamai irinsu Sheikh bin Baz sun nuna bidia ne “Addua’ul Jama’iy'” wato ai taro ai addua a Jama’ance (sai dai kowa yai tasa). Amma hakikanin gaskiya wannan ya kebanci addu’a bayan salatil maktubah, da filin Arfah, da lokacin dawafi, ta yanda wani yana addua wasu suna amsawa, da ma wasu wuraren, shi wannan baya ciki.
Amma, a daya bangaren, akwai Malamai da suka halatta “addu’aul Jama’iy'” in dai ba a mai da shi al’adah ba wacce za ai ta yi ko yaushe (“عادة متكررة). Daga ciki akwai Shaikhul Islam Ibn Taimiyyah, in da ya ce;
” Amma taruwar Jama’a su yi karatun Qurani suyi Zikri da adduoi wannan mustahabbi ne abin so, matukar ba a mai dashi al’adah ta ko yaushe ba عادة راتبة, sannan ba a raba shi da wata bidah abar ki ba بدعة منكرة,”.
(Majmu’ul Fatawa; 22/523)
An tambayi Imam Ahmad hukuncin taron Jamaa domin suyi dandazon karatun Qurani da addua da Zikri, sai ya bada amsa yace;
“Ba zan karhanta wannan ba ga Yan uwa sai dai idan sun yawaita yin hakan (ya zama aladarsu yawaita hakan).” Wannan kuma ita ce fatawar Ishaq bin Rahwiyah, Malamin Imamul Bukhari.
(Al-adab al-Shar’iyyah; 2/102)
A karshe nasiha ga daliban ilmi su rinka taka tsantsan wajen gaggauta fidda Fatawa domin kaucewa yin kuskure da jawowa malamai kalamai na rashin kimantasu daga masu karancin kima.
Allah ya zaunar da kasarmu lafiya.
Dr Ibrahim Ilyasu
7/08/24